Yobe: Gwamna Buni ya naɗa tsohon ɗan majalisar wakilai, Ismail Gadaka a matsayin sabon sarkin Gudi
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da nadin Hon. Ismail Ahmed Gadaka a matsayin sabon Sarkin Gudi, biyo bayan rasuwar marigayi Alhaji Isah Bunuwa Madugu.
Sanarwar nadin ta fito daga ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Yobe, inda aka bayyana cewa sabon nadin ya biyo bayan mutuwar tsohon mai rikon sarautar, wanda ya rasu bayan fama da doguwar rashin lafiya.
Kafin wannan nadin, Alhaji Ismail Ahmed Gadaka ya rike mukaman gwamnati da dama, ciki har da kasancewarsa ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Fika/Fune tsakanin 2011 zuwa 2019, da kuma Kwamishinan gwamnati a Jihar Yobe daga 2007 zuwa 2010. Har ila yau, ya rike sarautar Yariman Gudi kafin ɗaukaka zuwa matsayin Sarkin Gudi.
Nadin ya zo a daidai lokacin da ake ci gaba da maye gurbin sarakunan da suka rasu domin dorewar al’adun gargajiya a jihar.
Asalin Labari….Daily Nigeria Hausa

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
CP Azare Commends Peaceful Conduct of APC Primaries in Akwa Ibom
Kano South Fallout: Has Rurum Drawn a Red Line Against Kawu Sumaila?
When Ja’o’ji Answers Reconciliation With Humility in Victory
APC Aspirant Raises Concerns Over Conduct of Primary Election in Jigawa Constituency
Kano Govt Pledges Stronger Collaboration with FG, Partners on Education
Ambassador Dr Amina Umar Namadi Sponsors Mass Marriage for 300 Couples in Jigawa