By Auwal Bala
Hukumar tsabtace Sahihancin Magunguna da Abinci ta Ƙasa, NAFDAC ta ce shan maganin ƙarfin maza kan haifar da mutuwar fuju’a, ma’ana, mutuwar gaggawa.Hukumar ta ƙara da cewa magungunan karfin maza kan haifar da cutar ɓarin jiki inda maza za su riƙa shan su domin su burge matan da su ke saduwa da su.Darakta-Janar ta NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta yi wannan gargaɗin a saƙon ta na Kirsimeti da sabuwar shekara.Adeyeye ta nuna rashin jin daɗin ta game da yadda magungunan karfin maza su ka cika kasuwannin magani a faɗin ƙasar nan.A cewar ta, yawancin irin magungunan ma ba su da rijistar NAFDAC ɗin.“Shigo da su a ke yi ta ɓarauniyar hanya. Inda su na da rijista, to masu shigo da shi da masu sayarwa ba za su riƙa yin abin da su ke yi a kasuwanni, ka tuna, kafafen sadarwa da tituna ba,”Haka-zalika, wannan kiran na Adeyeye ya zo ne a lokacin da NAFDAC ta ce ta ƙwace jabun magunguna da kayan abinci da darajar su ta kai naira biliyan 3 a filin kasuwar bajakoli a Legas.

VICE PRESIDENT SHETTIMA OPENS WORLD PUBLIC RELATIONS FORUM 2026 IN ABUJA
Kano Govt Constitutes Committee to Investigate College of Nursing Sciences Management
APC Sports Mobilisation: 31 State Commissioners Adopt Grassroots Engagement Strategy Ahead of 2027
Shehu Dikko Leads Sports Mobilisation Drive as Youth Commissioners Endorse Tinubu’s Re-election
APC engages Kano stakeholders on Tinubu’s Renewed Hope Agenda
Defection, Dr. Mera Debunked Defection Rumour, Says Still In ADC And Kebbi North Senatorial Candidate
Senator Kawu Sumaila Commends Kano Drug Task Force, Donates ₦5m to Operatives, Supports Rescued Children
Nigeria’s Education System Needs Policy Consistency, Effective Implementation – Prof. Faruk Rashid Haruna
BPSR trains 660 federal officers on post-retirement productivity
Police Arrest Two Ekpo Masquerades Over Alleged Roadblock, Extortion in Akwa Ibom
Dangote Driving Agribusiness In North, Sponsors 2026 National Agric Show
Kano Taskforce Seals Pharmaceutical Company Over Alleged Illegal Distribution of Pregabalin