Menu

Hukumar Sadarwa ta Kasa NCC ta Kaddamar da Shirin Tantance Wayoyi don yakar Shigo da na Jabu

Admin 2 days ago 0

Hukumar Kula da Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta ƙaddamar da wani dandali na musamman mai suna *Device Checker Platform*, domin dakile yaɗuwar wayoyin hannu na jabu, waɗanda aka yi musu kwafi ko kuma ba su samu sahalewar hukuma ba a ƙasar.

Shirin na daga cikin matakan da hukumar ke ɗauka domin tabbatar da bin ƙa’idojin fasaha, kare haƙƙin masu amfani da wayoyi da kuma inganta tsaron hanyoyin sadarwa.

Mai kula da ofishin shiyya na hukumar NCC a Kano, Injiniya Maigana Gidado, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ofishin hukumar da ke Kano .

Ya ce dandamalin zai bai wa masu sayen wayoyi da sauran masu ruwa da tsaki damar tantance ko wayoyin da ke amfani da katin SIM sun samu sahalewar hukumar ta fuskar ingancin fasaha, kafin a saye su ko a shigar da su kasuwa.

A cewarsa, wannan mataki zai taimaka wajen tabbatar da gaskiya da bin ƙa’idoji a harkokin shigo da wayoyi, rarrabawa da sayar da su, tare da taimaka wa masu amfani da su wajen yanke shawarar da ta dace kafin saye.

Gidado ya bayyana cewa hukumar ta sauƙaƙa hanyoyin samun lasisi da daidaita matsayin masu sana’ar sayar da wayoyi, lamarin da ya ba da damar samun lasisi ga dimbin dillalan wayoyi a Jihar Kano.

Ya ƙara da cewa hukumar ta gudanar da shirye-shiryen wayar da kai ga masu shigo da wayoyi da sauran masu ruwa da tsaki a Legas da wasu sassan ƙasar domin ƙara fahimtar buƙatun samun sahalewar fasaha da kuma wajibcin bin ƙa’idojin da aka shimfiɗa a ƙarƙashin sabon tsarin.

Mai kula da ofishin shiyyar ya kuma bayyana cewa hukumar ta samar da manhaja mai sauƙin amfani, wadda za ta bai wa masu ruwa da tsaki da aka amince da su damar tantance lambar **IMEI** ta kowace waya da kuma ɗora bayanan da suka dace kai tsaye a kan dandamalin.

IMEI wata lamba ce ta musamman da ake amfani da ita wajen tantance wayar hannu.

Ya buƙaci masu sayen wayoyi da su tabbatar da sahihancin na’urar kafin saye, ta hanyar ziyartar shafin hukumar na **www.ncc.gov.ng/devicechecker**, inda za su yi amfani da lambar IMEI ta wayar domin gudanar da tantancewar.

Haka kuma, ya shawarci masana’antun wayoyi, masu shigo da su, masu rarrabawa da dillalai da su duba jagorar tantancewa da samun sahalewar na’urori ta hanyar **www.ncc.gov.ng/DeviceCheckerGuide**, domin fahimtar nauyin da ke kansu da kuma ƙa’idojin da ya kamata su bi.

Gidado ya jaddada cewa shirin Device Checker ba wani tsarin sa ido ne kan masu amfani da wayoyi ba, inda ya bayyana cewa dandamalin ba ya shiga bayanan sirri, saƙonnin waya, hotuna, lambobin abokan hulɗa, bayanan kuɗi ko wasu bayanai na sirri da aka adana a cikin wayoyi.

Ya ce manufar shirin ita ce tantance na’urori da kuma tabbatar da bin ƙa’idojin da suka shafi inganci da sahalewar su.

Hukumar NCC ta kuma buƙaci masu amfani da wayoyi da su riƙa saye daga amintattun dillalai masu lasisi, tare da tabbatar da ingancin wayoyin kafin saye domin kauce wa sayen na’urorin da ba su cika ƙa’idojin da aka shimfiɗa ba.

Haka kuma, ta yi kira ga masana’antun wayoyi, masu shigo da su, masu rarrabawa da dillalai da su tabbatar da cewa duk na’urorin sadarwar da suke shigarwa ko sayarwa a kasuwar Najeriya sun cika ƙa’idojin fasaha da hukumar ta gindaya.

Hukumar ta buƙaci masu buƙatar taimako ko waɗanda suke son shigar da ƙara da su kira layin kyauta na masu amfani da sabis ɗin sadarwa mai lamba **315**.

NCC ta sake jaddada aniyarta ta kare masu amfani da sabis ɗin sadarwa, tabbatar da gasa ta gaskiya, inganta tsaron hanyoyin sadarwa da kuma gina ingantaccen tsarin sadarwa da jama’a za su amince da shi a Najeriya.

Leave a Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *