Dakta Bashir Jamoh ya jajanta wa gwamnatin jihar Kaduna kan hare-haren da suka hada da titin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna da kuma mamaye filin jirgin sama na Kaduna wanda ya yi sanadin mutuwa da jikkata da kuma sace fasinjoji da ba a tantance adadinsu ba.
A wata wasika da ya aikewa Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, Jamoh, wanda kuma shi ne Darakta Janar na Hukumar Kula da Jiragen Ruwa ta Najeriya NIMASA, ya bayyana kaduwarsa da faruwar lamarin, yayin da ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasu da daukacin mutanen jihar Kaduna.
Allah (SWT) na nan tare da ku a wannan lokaci na alhini, muna kuma rokonSa da Ya samar da zaman lafiya, ci gaba da wadata a jihar Kaduna, in ji Jamoh.
Dokta Jamoh ya bukaci al’ummar Kaduna da su ci gaba da yin imani da Gwamnatin Jiha da ta Tarayya a kokarinsu na ganin an magance matsalolin tsaro da Jihar ke fuskanta.
Ya kara da cewa “Nagarta za ta rinjayi mugunta a koyaushe. Mu kasance masu lura a matsayinmu na ‘yan kasa nagari tare da sanar da jami’an tsaro da abin ya shafa abubuwan da suka shafi shakku ko abin da ba a gane masa a cikin jihar da kewaye.”

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
CP Azare Commends Peaceful Conduct of APC Primaries in Akwa Ibom
Kano South Fallout: Has Rurum Drawn a Red Line Against Kawu Sumaila?
When Ja’o’ji Answers Reconciliation With Humility in Victory
APC Aspirant Raises Concerns Over Conduct of Primary Election in Jigawa Constituency
Kano Govt Pledges Stronger Collaboration with FG, Partners on Education
Ambassador Dr Amina Umar Namadi Sponsors Mass Marriage for 300 Couples in Jigawa