Daga Adnan Abdullahi
Rundunar sojin ruwa ta Najeriya ta nada Commodore Aliyu Gaya a matsayin sabon kwamandan da ke tsaron teku na hukumar kula da harkokin jiragen ruwa ta Najeriya NIMASA. Commodore Aliyu Gaya ya maye gurbin Commodore Ezekiel Nyako Lamiri, wanda aka mayar da shi makarantar horas da sojoji ta Najeriya.
Har zuwa lokacin da aka nada shi, Commodore Gaya shi ne Daraktan rundunar hafaka ta kasashen yammacin Afrika ECOWAS dake sa ido kan ruwaye dake yankin na shiyyar Zone E dake Cotonou a jumhuriya Benin. Ya rike wasu mukamai na soja da kwamanda a cikin wasu rundunoni na sojojin ruwa daban-daban a ciki da wajen kasar nan.
Commodore Gaya ya yi digirin farko na Kimiyya a Chemistry da Digiri na biyu a Defence Management Command and Strategy. Har ila yau, yana da takardar shaida da ya samu a Cibiyar Koyar da Zaman Lafiya ta Duniya ta Koffi Annan dake Accra, Ghana.
Takarar Gwamnan Kaduna a 2023: Shugaban matasan Yarbawa ya bayyana halayen Dr. Jamoh
Ita dai rundunar dake samar sa tsaro kan ruwayen kasar nan ta samo asali ne daga Yarjejeniyar Fahimta da aka kulla tsakanin NIMASA da Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya don inganta dangantakar aiki ta kud da kut tsakanin sassan biyu na gwamnati wajen tabbatar da tsaron yankin tekun Najeriya.
Darakta Janar na NIMASA, Dr Bashir Jamoh, ya jaddada kudirin hukumar na ci gaba da yin hadin gwiwa da sojojin ruwa na Najeriya da sauran rundunonin sojin Najeriya domin tabbatar da tsaron iyakokin kasar da ma gabar tekun Guinea.
Dr Jamoh ya ce, “Hukumar a don haka ta yabawa Rundunar Ruwan Najeriya saboda mutunta wannan yarjejeniya na tura ƙwararrun jami’ai a koyaushe zuwa Hukumar Tsaron ruwa ta NIMASA tare da tabbatar da ingantaccen iyakokin ruwa don amfanin ƙasa da al’ummomin duniya.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
Governor Radda Distributes Subsidized Fertiliser across 6,652 Pollint Units
Police Order Joint Operations After Pirate Attack on Calabar–Oron Waterway
FG Intensifies Oversight of Kano–Zaria–Kaduna Rail Project
Shekarau Defect to APC After Consultations
Dropping Rurum for Deputy Governor: Gamble Gov Yusuf Cannot Afford – Analyst Warns