Menu

SHIRIN TSARE RUWAYEN KASA (DEEP BLUE PROJECT): KWAMITIN MAJALISA KAN RUNDUNAR SOJIN RUWA YA YABAWA HUKUMAR NIMASA.

Admin 4 years ago

… Shirin na kara samun tagomashi daga kasashen duniya.

Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai Mai Kula da Sojojin Ruwa na Najeriya Honorabul Yusuf Gagdi ya yabawa Hukumar Kula da Tsaro da sufurin jirage Ruwa ta Najeriya NIMASA bisa jajircewarta na nuna gaskiya da tsantsaini wajen aiwatar da ayyukan samar da tsaro na kasa baki daya kan RUWAYEN Kasa aka fi sani da Deep Blue Project. .

An yi wannan yabon ne a lokacin da Hukumar Gudanarwar Hukumar ta bayyana a gaban Kwamitin Majalisar Dokokin kan sha’anib sufurin Jiragen Ruwa a halin yanzu da ke binciken kwangilar shirin na Deep Blue da Najeriya ta baiwa kamfanin HLS International Limited kwangilar aiwatar da shi.

Ya ce: “Mu a Kwamitin Sojojin Ruwa muna yaba wa tawagar ku ta Hukumar NIMASA bisa samar da duk wasu takardu da muka nema. Ya nuna cewa ba ku da abin da za ku ɓoye”. Burinmu shi ne mu tabbatar da an kashe kudaden al’umma ba wai don amfanin jama’a kawai ba amma bisa tanadin dokokin kasa”.

Wani mamba a kwamitin Honorabul Alao Ajala ya bayyana jin dadinsa kan yadda Najeriya ta fita cikin jerin kasashe 010masu fashin teku a duniya. Wannan na zuwa ne bayan da galibin mambobin kwamitin suka yabawa rundunar sojin ruwa bisa tsayuwar daka wajen inganta tsaro a kan iyakokin ruwan kasar nan.

A jawabinsa ga kwamitin, Babban Daraktan NIMASA Dr Bashir Jamoh ya ce Hukumar ta yi aiki ne bisa amincewar Majalisar Zartarwa ta Tarayya domin Hukumar ta tallafa wa aikin Deep Blue a kan dalar Amurka miliyan 195 tare da kudin gudanarwa na kashi 10%,  inda ya ƙara da cewa kudaden da aka kashen sun samu amincewa na majalisar Kasa.

Zamu kara inganta alakar aiki tsakanin NIMASA da Makarantar kimiyya da fasaha da lamuran sufurin jiragen ruwa – Dr Bashir Jamoh

Har ila yau, ya bayyana cewa gwamnatin Koriya ta yi na’am da Shirin Deep Blue “Gwamnatin Koriya ta yi farin ciki da manufar shirin Deep Blue Project kuma ta yi alƙawarin tallafawa Najeriya ta hanyar ba da gudummawar jirgin ruwa don ƙara yawan jiragen ruwa a ƙarƙashin aikin. Gwamnatin Japan ta kuma shiga ta hanyar yin alkawarin tallafawa ta hanyar kudade. “

Dr Jamoh ya lissafo irin kayayyakin aikin da NIMASA ta samu don aiwatar da shirin da suka hada da jiragen ruwa na ko-ta-kwana guda 17, jiragen ruwa na musamman guda 2, jiragen sama na musamman guda 2, jiragen sama masu saukar ungulu 3 da jiragen sama marasa matuka guda 4 da motocin sulke guda 16. Har ila yau, aikin yana da umurni da cibiyar kulawa da aka fi sani da C4i Center da ke cikin cibiyar NIMASA a Lagos wanda haɗin gwiwar jami’ai daga dukkan rundunonin sojojin Najeriya, ma’aikatan NIMASA da sauran Hukumomin soji waɗanda ke cikin aikin. .

Kayayyakin aikin mallakar hukumar ne da ke hannun jami’an soji daban-daban na gwamnati don inganta tsaro na jigilar kayayyaki a yankin tekun Najeriya.

A wani labarin kuma, Mai girma Ministan Sufuri, Honarabul Rotimi Amaechi ya bayyana cewa Najeriya ta samu karramawa daga kasashen duniya ta hanyar samun lambar yabo daga kungiyar Tarayyar Afirka kan shirin Deep Blue Project.

Da yake magana a ranar Talata, a zaman Kwamitin Majalisar Wakilai kan Rundunar Sojan Ruwa game da binciken shirin Deep Blue Project   da aka bada Kwangilar ga HLS International Limited, Ministan Sufurin ya ce an sami amincewar da suka dace kafin aiwatar da aikin Deep Blue.

Ya ce, “Na kasance a Nairobi a makon da ya gabata, yayin da kungiyar Tarayyar Afirka ta ba mu lambar yabo kan shirib Deep Blue Project. A halin yanzu, yawan laifuffuka a ruwanmu da yankin gabar tekun Guinea ya ragu. Kafin yanzu, mun sahub gaba a duniya, amma, tun lokacin da aka tura aikin HLSI, fashin teku ya ragu matuka.”

Osagie Edward
Mataimakin Darakta, Hulda da Jama’a na Hukumar NIMASA
edward.osagie@nimasa.gov.ng
16 ga watan Maris, 2022