Darakta Janar na Hukumar Kula da Tsaro da sufurin jiragen Ruwa ta Najeriya, NIMASA, Dr. Bashir Jamoh ya zama wanda ya lashe lambar yabo ta hazikin ma’aikacin gwamnati a bangaren sufurin jiragen ruwa na gidan jaridan vanguars wato (Vanguard Public Sector Icon, Maritime, 202).
Editan Jaridar Vanguard, Mista Eze Anaba wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da takardar isarwa ga Dr Jamoh a Legas ya ce sauran wadanda aka karrama sune Shugaban Bankin Raya Afirka, Akinwunmi Adesina, shugaban kamfanin mai na kasa NNPC, Mele Kyari, da Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo da dai sauransu.
Mista Anaba ya yi nuni da cewa, kwamitin tantance wadanda za a karrama na jaridar ta Vanguard sai da Yayi nazari mai zurfi kafin zaben sunan Dr. Jamoh da bayan dogon bincike aka gani cewa shugaban hukumar ta NIMASA shi ne fitaccen jami’in gwamnati a shekarar 2021.
Ya lura da cewa kwarewa ta Dokta Jamoh a shugabancin hukumar NIMASA ya sa aka samu sauyi a fuskar sufurin jiragen ruwa a Nijeriya. Ya kara da cewa, duk da cewa NIMASA ba hukumar samar da kudaden shiga ba ce ta gwamnati, amma duk da haka hukumar bisa sa idon Jamoh, ta toshe kafofin da kudin suke sulalewa tare da Tarawa gwamanti kudin da suka kai Naira Biliyan 37 a kowane lokaci-kudin da ba a taba Tara su ba gabanin zuwa Jamoh.
Hakazalika, Hukumar kula da harkokin teku ta duniya IMB a ranar 3 ga Maris, 2022 ta sanar da cire Najeriya daga jerin masu fashin teku a duniya sakamakon ci gaba da raguwar ayyukan sata a tekunan Najeriya. Sakatare Janar na Hukumar Kula da sufurin Jiragen Ruwa ta Duniya, IMO, Kitack Lim, a yayin taron Kwamitin Kare Ruwa a makon da ya gabata, ya amince da Nijeriya kan ci gaba da tsamun ci gaba a yaki da masu fashin teku a mashigin tekun Guinea, ya kuma yaba wa hadin gwiwar da ke tsakanin sassan yankin a kokarin samun ingantacciyar tsaro kan dakon kaya a teku.
Jim kadan bayan samun sanarwar karramawar, Dr. Jamoh ya yabawa wadanda suka shirya wannan karramawar tare da nuna cewa yanzu an zaburar da shi ne domin ninnika irin kwazon da yake nunawa wurin hidimar al’umma.
“Wannan sanarwa da ke fitowa daga sanannen Gidan jarida kamar ta “Vanguard kira ne don yin ƙarin hidima. Tun ranar 3 ga Maris, lokacin da IMB ta fitar da Najeriya daga jerin kasashe da ake fama da masu gashi a teku a duniya, ya zame mana sabon aikin dake gaban shi ne dorewar wannan Nasara da aka samu. Za mu ci gaba da haɗin gwiwa tare da duk masu ruwa da tsaki a cikin gida da waje don tabbatar da ci gaba mai dorewa na bangaren sufurin ruwa a Najeriya. “Ya ce.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
CP Bello Inspects Police Constables Screening Exercise in Gusau
Police Repel Bandit Attacks in Maru, Bukkuyum LGAs of Zamfara
NUJ Kebbi Condoles Gov Idris K/HA Members, Zuru Emirate On The Passing Of Speaker MUHAMMAD USMAN ZURU
Police Arrest Motorcycle Theft Suspect, Recover Stolen Bajaj Boxer in Kano
Catholic Diocese Calls on Federal, Kebbi Govts To Restore Security in Shanga