Hukumar Kula da Tsaro da sufurin jiragen Ruwa ta Najeriya NIMASA ta samu gudummawar dalar Amurka miliyan 2.4 (kimanin N994.8m) daga gwamnatin Japan don tallafawa ayyukanta na Deep Blue Project sake tabbatar da tsaro a rueayen kasar nan.
Har ila yau, ta samu wani gudunmuwar wani jirgin ruwan yaki da za ta kara a cikin jiragenta daga gwamnatin Koriya.
Darakta Janar na hukumar, Dr Bashir Yusuf Jamoh ne ya bayyana hakan jiya a wata hira da manema labarai a Zariya.
Ya bayyana cewa, shirin Deep Blue Project wanda aka fi sani da Integrated National Security and Waterways Protection Infrastructure, Ma’aikatar Sufuri da Ma’aikatar Tsaro ta Tarayya ne suka kaddamar da shi a yayin da NIMASA ke aiwatarwa.
“Shirinmu na Deep Blue Project da Dokar nan ta SPOMO da Majalisar Dokoki ta Kasa ta samar, da hukuncin daurin rai da rai a karkashin dokar SPOMO, da jajircewar sojojin ruwa na Najeriya da sauran rundunonin soji na Sojojin Najeriya, ba tare da mantawa da goyon bayan kasashen duniya ba, duk sun haifar da raguwar masu fashib teki a mashigin tekun Guinea,” in ji shi.
A halin da ake ciki, Dr Jamoh ya ce nan ba da jimawa ba za a fara amfani da tashar jirgin ruwa na hukumar domin tsayawa da saukar fasinja. Jamoh ya bayyana haka ne a lokacin da yake karbar bakuncin tawagar Jami’ar Maritime ta Najeriya (NMU) wadanda suka ziyarci hukumar ta NIMASA a Legas.
Shugaban ya yi bayanin cewa kwararru daga masu kera jirgin ruwan sun kwashe sama da wata guda a Najeriya suna aiki a kan yadda wannan tasha za ta fara aiki.
“Lokacin da na ba su wa’adin gaggauta kammala aikin , an ba ni shawarar kwararrun da kada in yi gaggawa. Idan mun dau tsawon wannan lokaci, za mu iya jira na wani lokaci kuma mu tabbatar ba mu yi nadama ba kan wannan muhimmiyar tasha , ”in ji DG.
Ya kuma sanar da hukumar jami’ar ta NMU cewa wurin zai kasance ga daliban jami’a don kwarewa a aikace idan ya fara aiki.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
CP Bello Inspects Police Constables Screening Exercise in Gusau
Police Repel Bandit Attacks in Maru, Bukkuyum LGAs of Zamfara
NUJ Kebbi Condoles Gov Idris K/HA Members, Zuru Emirate On The Passing Of Speaker MUHAMMAD USMAN ZURU
Police Arrest Motorcycle Theft Suspect, Recover Stolen Bajaj Boxer in Kano
Catholic Diocese Calls on Federal, Kebbi Govts To Restore Security in Shanga