Babban Daraktan Ƙungiyar APC Media and Mobilization Group for Ahmed Bola Tinubu (ABT) na shiyyar Arewa maso Yamma Amb. Aminu Nuruddeen Amin ya miƙa takardun kama aiki ga Hon. Tijjani Sani Amasko da Hon. Kabiru Aluta Dambatta a matsayin director da Secretary na jihar Kano a madadin shugaban ƙungiyar na ƙasa Comrade Kingsley Omadoye.
Amb. Aminu yace bai yi wannan zaɓi da ka ba sai da yayi zuzzurfan bincike sannan ya gano cewa babu wasu jajirtattun matasa a jihar Kano waɗanda suka shahara wajen tallata jam’iyyar APC da ƴan takarkarinta na kowanne mataki kamar Tijjani Sani Amasko da abokan aikin sa. Ya tabbatar da cewa idan suka karɓi abu to sunayi da gaske, kuma suna da tsayayyen tsarin da duk saƙon da suka karɓo zasu aikashi kuma zai dire har ƙasa kasancewar suna da tsarin da ya taho daga jiha, shiyya zuwa ƙananan hukumomi ya tafi har mazaɓu.
Amb. Aminu Nuruddeen a madadin shugabanninta na ƙasa ya tabbatar da cewa wannan ƙungiya tana biyayya sau da ƙafa ga jigo a tafiyar Tinubu wato Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, kuma tuni yana cikin iyayen wannan ƙungiya na Arewa Maso Yamma.
A ƙarshe, An bayar da shawarwari tare da addu’ar Allah S.W.T ya bawa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin sa Sen. Kashim Shettima nasara a zaɓen 2023 mai zuwa, Ameen.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
CP Bello Inspects Police Constables Screening Exercise in Gusau
Police Repel Bandit Attacks in Maru, Bukkuyum LGAs of Zamfara
NUJ Kebbi Condoles Gov Idris K/HA Members, Zuru Emirate On The Passing Of Speaker MUHAMMAD USMAN ZURU
Police Arrest Motorcycle Theft Suspect, Recover Stolen Bajaj Boxer in Kano
Catholic Diocese Calls on Federal, Kebbi Govts To Restore Security in Shanga