Shugaban hukumar kula da iyakokin ruwan kasar nan Dr Bashir Yusuf Jamoh yace kudirin inganta ayyukan ma’aikatan jiragen ruwa na gaban majalisar dokoki na kasa don yin muhawara.
A wata sanarwar da ta samu sa hannun mataimakin darakta a sashin hulda da jama’a na hukumar, Mr Edward Osagie ta ce, Dr Bashir Yusuf Jamoh ya bayyana hakan ne a wajen taron kaddamar da majalisar hadin gwiwa na masana’antu na kasa don yin bitar hanyoyin inganta ayyukan ma’aikatan jiragen ruwa wanda ya gudana a ofishin NIMASA dake birnin ikko.
A cewar Dr Bashir Yusuf Jamoh, taron bitar ya zo akan gaba saboda ya zo a daidai lokacin da ake kokarin an shigar da sakamakon bitar cikin muhawarar da majalisar za tayi nan ba da jimawa ba.
Yayi nuni da cewa taron yana da matuqar muhimmanci don tattauna yanda za a samar da isashshen diyya, albashi, kyakkyawar yanayin aiki ga ma’aikatan, da kuma tabbatar da cewa ma’aikatu sun dauki alhakin cike sharuddan aiki daidai da na zamani.
Idan za a iya tunawa dai, a kwanakin baya hukumar NIMASA ta jagoranci tattaunawa da majalisar hadin gwiwa na masana’antu na kasa, da kungiyar ma’aikatan iyakokin ruwan kasar nan da kuma masu ruwa da tsaki don tattaunawa akan batun karin albashi da sauran haqqoqin ma’aikatan.
A nashi tsokacin wurin taron, Daraktan ma’aikatan kwadago a hukumar, Injiniya Victor Ochei yace taron bitar zai amfani dukkan ma’aikatan kula da harkokin iyakokin ruwan kasar nan.
Ya lura da cewa taron bitar zai kuma inganta kyakkyawar alaqar aiki tsakanin ma’aikata da masu ruwa da tsaki a harkar kula da iyakokin ruwan kasar nan.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
CP Bello Inspects Police Constables Screening Exercise in Gusau
Police Repel Bandit Attacks in Maru, Bukkuyum LGAs of Zamfara
NUJ Kebbi Condoles Gov Idris K/HA Members, Zuru Emirate On The Passing Of Speaker MUHAMMAD USMAN ZURU
Police Arrest Motorcycle Theft Suspect, Recover Stolen Bajaj Boxer in Kano
Catholic Diocese Calls on Federal, Kebbi Govts To Restore Security in Shanga