Babban Sakataren hukumar kula da iyakokin ruwa na duniya, Mr Kitack Lim ya kaddamar da sabon ginin shedikwatar NIMASA na zamani dake yankin Victoria Island a jihar Legas.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da sabon ginin, Mr Kitack Lim ya bayyana gamsuwar shi bisa jagorancin Ministan harkokin sufuri, Injiniya Mu’azu Jaji Sambo da sauran shugabannin hukumomin dake karkashin ma’aikatar shi.
Ya kuma jinjina kokarin da aka yi wajen samar da sabon ginin, sannan ya jaddada muhimmancin inganta kwarewar ma’aikata don cimma manufar da aka sanya a gaba.
Shima a nashi jawabin, Ministan harkokin sufuri, Injiniya Mu’azu Jaji Sambo ya godewa babban sakataren dangane da ziyarar da ya kawo Nijeriya don ganewa idanun shi irin cigaban da aka samu a bangaren iyakokin ruwan kasar nan.
KARANTA WANNAN:SHUGABAN HUKUMAR NIMASA YA JINJINAWA MASU RUWA DA TSAKI
Ya kuma bada tabbacin cewa Nijeriya za ta cigaba da aiwatar da manufofin bangaren ta na iyakokin ruwa daidai da na zamani ta hanyar yin amfani da kimiyyar da fasaha.
A nata tsokacin, Shugabar kwamitin majalisar wakilai akan iyakokin ruwa, Misis Lynda Ikpeazu ta yaba da salon jagorancin Shugaban hukumar NIMASA, Dr Bashir Jamoh sannan ta bukaci da ya kara bada himma wajen ciyar da hukumar gaba.
Shugaban hukumar ta NIMASA, Dr Bashir Yusuf Jamoh ya bayyana farin cikin shi ne bisa ziyarar Mr Lim inda ya sanar da shi cewa hukumar ta dukufa wajen ganin ta samar da kyakkyawar yanayi a bangaren kula da iyakokin ruwan kasar nan tare da goyon bayan masu ruwa da tsaki a bangaren.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
From Corruption to Cannabis: As Governor Yusuf Puts Muhiyi, Anti-Graft Czar, in Charge of Kano Drug Crackdown
STATE POLICE IN NIGERIA: UNDERSTANDING THE TRUE POSITION OF THE PROPOSED CONSTITUTIONAL FRAMEWORK
NAWOJ, NGOs take anti-drug campaign to Kano streets
Katsina Secures Fresh $8m World Bank Support
MEMBER SUMAILA/ TAKAI DESCRIBES GOVERNOR ABBA KABIR YUSUF AS A WORKAHOLIC LEADER
Investing in Community Health Key to Northern Nigeria’s Development – Expert