Menu

Yajin aikin masu hayar keke Napep: Masu sana’ar Achaba na cin kasuwa a Kano

Admin 4 years ago

Tun bayan tsunduma yajin aikin da masu hayar babur Mai kafa uku wato adaidaita sahu a kano alummar da ke birni da kewaye sun fada cikin halin kaka nikayi sakamakon rashin abin hawa da yayi karanci.
Wakilin time express wanda ya kewaya birni da kewaye yaga alumma na tafiya a kasa daga wannan unguwa zuwa wancan inda masu sana’ar Achaba ke ta cin kasuwa ba kakkautawa.

Hassada da kyashi su ne jigon rashin cigaba a Afrika – Farfesa Gwarzo

Jami’an Tsaro sun yi Ram da ‘Yan fashin daji a zamfara
Su dai masu haya da baburan adaidaita sahun sun taunduma yajin aikin ne sakamakon korafin da suke yi na cewar kidin izinin yin haya da babur din na naira dubu takwas da gwamnati ta sanya ya yi musu yawa, kuma sunyi zargin cewar jamian karotan na uzura musu.
A zantawarsa da manema labarai shugaban hukumar ta Karota Baffa Babba Dan’agundi yace babu gudu ba ja da baya kan batun biyan kudin.