Menu

AZMAN YA KADDAMAR DA SABON GIDAN SAI DA MAN FETUR NA ZAMANI A ABUJA, 28 ga Satumba, 2026

Admin 2 hours ago 0

 

Kamfanin Rukunun Azman ya kaddamar da wani sabon katafaren gidan sayar da man fetur na zamani a yankin Nyanya Checkpoint/Mopol Junction da ke Abuja, a wani mataki na fadada samar da ingantattun kayayyakin man fetur da kuma inganta ayyukan da yake yi wa al’umma.

Da yake jawabi a wajen bikin kaddamarwar, Mataimakin Shugaban Zartarwa na Azman Ambasada Alhaji Mustapha Abdulmunaf Yunusa Sarina Baraden Gaya, wanda ya wakilci wanda ya kafa kamfanin, ya ce sabon gidan man zai saukaka wa jama’a samun man fetur da sauran kayayyakin da kamfanin Azman ke samarwa.

Ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da amfani da sabon gidan man, tare da tabbatar musu da cewa za a samar da ingantattun kayayyaki da kuma kyakkyawan tsarin hidima ga kwastomomi.

Mataimakin Shugaban Zartarwar ya kara da cewa, Azman na ci gaba da jajircewa wajen samar wa jama’a da ingantattun ayyuka, tare da kiyaye ka’idojin kwarewa da kuma gamsar da kwastomomi.

A nasa jawabin, Babban Manajan Azman Group of Companies, Ambasada Alhaji Mukhtar Ibrahim, ya bayyana godiya ga abokan huldar kasuwanci na kamfanin, hukumomin gwamnati, kwastomomi da sauran jama’a da suka halarci bikin kaddamarwar.

Ya ce bude sabon gidan man Azman wani karin ci gaba ne da ke nuna yadda Azman Group of Companies ke ci gaba da habaka da fadada ayyukansa.

Daya bayan daya, baki da masu ruwa da tsaki da suka halarci taron sun yaba da wannan shiri, tare da jaddada muhimmancin samun ingantaccen tsarin samar da man fetur ga masu ababen hawa da mazauna yankin.

Haka kuma, bikin ya samu halartar wakilan hukumomin tsaro da na agajin gaggawa, ciki har da Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC), Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, da Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, da kuma Hakimin Nyanya, Mai Martaba HRH, tare da sauran masu ruwa da tsaki.

Ana sa ran sabon gidan man na Azman zai saukaka wa mazauna Nyanya, masu ababen hawa da ’yan kasuwa samun man fetur cikin sauki, musamman wadanda ke zaune ko gudanar da harkokinsu a Nyanya da kewayenta.

Leave a Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *