Menu

NIMASA ta dauki nauyin gasar rubutun zube don tunawa da ranar sufuri ruwa ta duniya

Admin 4 years ago

Daga Abdullahi Kano

Hukumar Kula da Kare sufurin jiragen Ruwa ta Najeriya (NIMASA) ta shirya gasar rubutun zube don tunawa da ranar sufurin jiragen ruwa ta duniya ta 2021 mai taken “Matuka jiragen ruwa sune alkadari ga makomar sufurin jiragen ruwa a nan gaba”.

An shirya gasar rubutun ne domin wayar da kan jama’a game da damarmaki dake tattare da fannin sufurin ruwa da kuma kwadaitar da matasan Najeriya da su zo a dama da su don cin wannan gajiya.

Hukumar kula da sufurin jiragen ruwa ta duniya (IMO) da kuma sauran kasashe mambobinta suka kebe ranar tunawa da sufurin jiragen ruwa ta duniya don mai da hankali kan mahimmancin jigilar kayayyaki, bada tsaro ga ruwaye, ma’aikatan jirgin ruwa da sauran takamaiman abubuwan da ke cikin aikin wannan hukuma ta IMO.

MAUDU’IN DA ZA A YI GASAR RUBUTUN ZUBE A KANSA

Maudu’in shine Matuka jiragen ruwa sune alkadari ga makomar sufurin jiragen ruwa a nan gaba kamar yadda Hukumar kula da sufurin jiragen ruwa ta duniya (IMO) ta sanya a taken bikinta na bana.

DOKOKIN SHIGA GASAR
*Gasar a buɗe take ga ɗalibai dake shekara ta 1 da ta 2 kacal na manyan makarantun Najeriya.

  • Ana buƙatar masu shiga gasar su aiko rubutun da suka yi tare da takardun shaida cewa su dalibai ne
    *Tabbacin ya ƙunshi wasiƙar bada gulbin shiga Makaranta(admission letter) da Katin shaida na Makaranta (ID card) kuma za a tura ne ta wannan adireshi wmdessay@nimasa.gov.ng ko kuma mail@samuelson.com.ng.
  • Rubutun da za a yi kar wuce kalmomin 1200 kuma girman rubutun ya kasance 12 (12 font size) tare da yin double spacing.
  • Ba za a karbi aikin da aka kwafa daga wani ba.
  • A karshen rubutun zuben ana so ya kare ne kumshe da lambar tarho da adireshin imel na masu shiga GASAR.
  • Duk rubutun da ya saba da Wadan nan ka’idoji ba za a karba ba
  • Wadanda suka yi nasara ne kawai za a tuntuba.

KYAUTUTTUKA
MATSAYI NA FARKO: Tallafin Ilimi na N500,000 da kwamfutar tafi-da-gidanka, da wallafa rubutun da ya ci nasara a cikin Mujallar NIMASA ta The VOYAGE da kuma dorawa a sashin gidan yanar gizon NIMASA.

MATSAYI NA BIYU: Tallafin ilimi na N350,000 da kyautar kwamfutar tafi-da-gidanka.

MATSAYI NA UKU: Tallafin ilimi N250,000 + kwamfutar tafi-da-gidanka

LOKAYI DA ZA A YI GASAR

Ranar litinin, 14 ga watan Maris, ya zuwa ranar lahadi , 3 ga watan Afrilu, 2022.
A tuna cewa duk rubutun da aka gaza turowa Kafin cikar wa’adin da aka diba ba za a karba ba.

RANAR BADA KYAUTUKA GA WADANDA SUKA YI NASARA

Za a sanar da wadanda suka yi Nasara makonni biyu bayan cikar wa’adin gasar.
Daga bisani za a sanar da ranar karban kyauta

Wanda ya shirya
SAMUELSON

Ita kuma hukumar kula da harkokin sufurin jiragen ruwa ta Najeriya NIMASA ta dauki nauyi.

Sanarwa daga mahukumta

NIMASA TA SAMU SABON KWAMANDAN KULA DA RUWAYEN KASAR NAN