An kira da iyaye su kara dagewa wajan Taimakawa Makarantun islamiyyu da na Karatun Allo don cigaban ilmi baki daya.
Wannan kira ya futo data Marafan Madakin Kano a wajan Saukar Karatun Al’kur’ani na Dalibai guda (20) a makarantar koyan Addini da Ilimin Al’alku’ani ta Unguwar Diso, dake karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano.
Alhaji Bashir Idris Diso ya yi dogon Bayani akan Hakkin Iyaye akan Yayansu da kuma Hakkin Yaya akan iyayensu.
Mai girma marafan madakin kanon ya kara da yabawa Malaman makarantun Islamiyyoyi da makarantun Allo, yada suke kokari wajan zaburar da Dalibai gun Illimin Addini,Ya kuma kira da masu Hali dasu dinga Tallafawa irin Wadannan makarantun da kayan Karatun,abubuwan zama, da Shawarwari Dan ganin an samu Nasarori wajan gudanar da karatuttuka a makarantun.
Shima a Nashi Jawabin Shugaban Makarantar Alh. Shu’aibu Mas’ud ya godewa malaman makarantar bisa kokarinsu da kuma Sha’awarsu wajan ganin makarantar ta ci gaba.
Shima a mashi jawabin Mai’unguwar Diso, Alh. Ahmad Bello Diso, ya godewa Matasan da ke yankin bisa kokarinsu na naiman ilimi da kuma kauracewa Rudin Duniya da sauran Futunu a yankin. Haka kuma, wani Dattijo Alh. Abdulkadir Hassan ya godewa daukacin Mahaddatan, tare da fatan su kara dagewa wajan tulawa da sauran karatattukansu Littattafan Addini.



Pantami Ta Tsaya Cak Yayin Da Dubban Jama’a Sukayi Tururuwar Tarbar Jamil Gwamna
AZMAN YA KADDAMAR DA SABON GIDAN SAI DA MAN FETUR NA ZAMANI A ABUJA, 28 ga Satumba, 2026
Naja’atu Muhammad; Pantami nada Suffar Munafikai
Zaben Gwamna A Gombe: Dalilan da Ya Sa Sardaunan Gombe Ya Zama Mafi Sauƙin Ɗan Takarar Gwamna da Za a Gabatar wa Jama’a
Amincin Tinubu Ga Barau Kan Harkar Tsaro Da Cigaban Kasa
Shugaban Ƙaramar Hukumar Kabo Hon. Lawan Najume Kabo ya sauke Sakataren Mulki na Karamar Hukumar da nadaddun Kansiloli huɗu, Saboda Shiga Ƙungiyar Tallata Shugaba Tinubu Da Sanata Barau (TMS) a Jihar Kano .
Nigeria, Russia Strengthen Customs Cooperation to Optimise Trade Facilitation, Information Exchange
NCoS Promotes 132 Officers in Kano, Controller Charges Beneficiaries on Professionalism
Senator Kawu Sumaila Commends Kano Drug Task Force, Donates ₦5m to Operatives, Supports Rescued Children
Nigeria’s Education System Needs Policy Consistency, Effective Implementation – Prof. Faruk Rashid Haruna
BPSR trains 660 federal officers on post-retirement productivity
Police Arrest Two Ekpo Masquerades Over Alleged Roadblock, Extortion in Akwa Ibom