Menu

Hukumomi a Kasar Saudiyya sun bayyana cewa aƙalla mutane miliyan daya ne za su gudanar da ibadar aikin hajjin bana.

Admin 4 years ago

daga Mukhtar Khalil

Rahotanni sun bayyana cewarma’aikatar aikin hajji da Umara ta kasar ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar ,wadda ta bayyana sharudda da za’ai amfani da su yayin ibadar.

Sanarwar tace hukumar ta amince mutane miliyan daya daga ciki da wajen Kasar su gudanar da aikin hajjin, Amma bisa sharadin bin matakan kare kai daga annubar Covid-19, wadda ita ta hana gudanar da ibadar a Shekarun 2020 da 2021.

Daga cikin sharuɗɗan ma’aikatar ta ce bazata bari dattawan da suka haura Shekaru 65 a duniya su gudanar da ibadar ba a bana, Sannan suka ce duk wanda zai shiga Kasar sai an yi masa gwajin Corona na aƙalla kwana biyu kafin ya shiga kasar ta Saudiyya.

Sanarwa ta kara da cewa dole ne duk maniyata aikin hajji bana sai an yi musu allurar rigakafin Covid-19 wadda kasar Saudiyya ta amince da ita, da kuma bin sauran matakan kula da Lafiya kamar yadda aka saba.

Idan ba a mantaba Kadaura24 ta rawaito Shekaru biyu kenan annubar Covid-19 tana hana gudanar da aikin hajji da mutane Masu yawa a duniya.