Kotun ɗaukaka ƙara da ke Kano a yau Laraba ta yi watsi da hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta Kano ta yanke tare na wanke mai neman takarar gwamnan Kano, Abdulsalam Abdulkarim Zaura wanda aka fi sani da A. A Zaura.
Solacebase ta ruwaito cewa hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC ce ta gurfanar da A. A Zaura a gaban babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano bisa tuhume-tuhume biyar.
Hukumar ta zargi Zaura da damfarar wani ɗan kasar Kuwait kuɗi Dalar Amurka miliyan ɗaya da dari uku da ashirin bisa zargin cewa yana sana’ar gine-gine a Dubai da Kuwait da sauran ƙasashen Larabawa.
A ranar 9 ga Yuni, 2020, Mai shari’a Lewis Allagoa ya sami wanda ake tuhuma ba shi da laifi kuma ya sallame shi kan dukkan tuhume-tuhumen.
A bisa rashin gamsuwa da hukuncin da karamar kotun ta yanke, Lauyan da ke kare masu kara Musa Isah ya shigar da ƙarar a kotun ɗaukaka ƙara a wani yunƙuri na soke hukuncin da karamar kotun ta yanke.
A wani mataki na bai daya da wasu alƙalan kotun ɗaukaka ƙarar guda uku suka yanke kuma mai shari’a Abdullahi M. Bayero ya sanar da hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke.
Bayero ya bayar da umarnin a sake yi wa wanda ake ƙara shari’a bisa jagorancin wani alkali na daban ba Justice Allagoa ba.
Babban abin da ake ta cece-kuce a cikin ɗaukaka ƙarar shi ne wanda ake tuhuma bai halarci kotun ba a lokacin da aka yanke hukuncin kuma bisa wasu hukunce-hukuncen da kotun kolin ta yanke, an ce wanda ake tuhuma dole ne ya kasance a gaban kotu a duk tsawon shari’ar da ake yi masa ciki har da yanke hukunci.
A kan haka ne kotun ɗaukaka ƙara ta samu ikon karɓa tare da yin watsi da hukuncin baya.
“Bayan an tantance batun don goyon bayan wanda ya shigar da ƙara, a dabi’ance karar ta yi nasara, An soke ƙarar mai lamba FHCK/CR2018/FRN wadda aka shigar kan Abdulsalam Sale Abdulkarim wanda aka yanke hukuncin ranar 9 ga watan Yuni, 2020.”
Bayero ya kuma bayar da umarnin a mayar da shari’ar zuwa babbar kotun tarayya a sake fara shari’ar.
Asalin labari…..jaridar solacebase

Pantami Ta Tsaya Cak Yayin Da Dubban Jama’a Sukayi Tururuwar Tarbar Jamil Gwamna
AZMAN YA KADDAMAR DA SABON GIDAN SAI DA MAN FETUR NA ZAMANI A ABUJA, 28 ga Satumba, 2026
Naja’atu Muhammad; Pantami nada Suffar Munafikai
Zaben Gwamna A Gombe: Dalilan da Ya Sa Sardaunan Gombe Ya Zama Mafi Sauƙin Ɗan Takarar Gwamna da Za a Gabatar wa Jama’a
Amincin Tinubu Ga Barau Kan Harkar Tsaro Da Cigaban Kasa
Shugaban Ƙaramar Hukumar Kabo Hon. Lawan Najume Kabo ya sauke Sakataren Mulki na Karamar Hukumar da nadaddun Kansiloli huɗu, Saboda Shiga Ƙungiyar Tallata Shugaba Tinubu Da Sanata Barau (TMS) a Jihar Kano .
Senator Kawu Sumaila Commends Kano Drug Task Force, Donates ₦5m to Operatives, Supports Rescued Children
Nigeria’s Education System Needs Policy Consistency, Effective Implementation – Prof. Faruk Rashid Haruna
BPSR trains 660 federal officers on post-retirement productivity
Police Arrest Two Ekpo Masquerades Over Alleged Roadblock, Extortion in Akwa Ibom
Dangote Driving Agribusiness In North, Sponsors 2026 National Agric Show
Kano Taskforce Seals Pharmaceutical Company Over Alleged Illegal Distribution of Pregabalin