A yayin da Nijeriya ta shiga sahun sauran kasashen duniya wajen bikin ranar iyakokin ruwa na duniya, Ministan harkokin sufuri, Mu’azu Jaji Sambo ya ce a shirye Nijeriya take wajen cimma muradan karni a bangaren iyakokin ruwa.
A sanarwar da mataimakin darakta a sashin hulda da jama’a na hukumar NIMASA Mr Edward Osagie ya fitar, Ministan yace ba za a bar Nijeriya a baya ba wajen inganta harkar sufurin jiragen ruwa a fadin duniya ba, inda ya bukaci masu ruwa da tsaki a bangaren da su bullo da dabarun inganta sufurin jiragen ruwa.
A nashi bangaren, Shugaban hukumar kula da iyakokin ruwan kasar nan-NIMASA, Dr Bashir Yusuf Jamoh yace taken bikin ranar iyakokin ruwan na bana yayi daidai da burin hukumar na samar da kyakkyawar yanayin sufurin jiragen ruwa a Nijeriya inda yayi nuni da cewa Nijeriya na sahun gaba wajen kira ga kasashe da su amsa kiran Sakatare Janar na hukumar kula da iyakokin ruwan duniya Kitack Lim ga kasashe masu tasowa na amfani da sabuwar tsarin sufurin jiragen ruwa na zamani.
A cewar Kitack Lim sabbin tsare-tsare da dabaru na zamani na inganta sufurin jiragen ruwa na da nufin tafiya tare da kowa bayan farfadowa daga annobar cutar kwaronabairos da ya mamaye duniya.
A matsayin Nijeriya ta mamba a kungiyar kula da iyakokin ruwa na duniya ta hanyar wakilcin NIMASA, Nijeriya shaida ce a yarjejeniyoyin kare muhalli daga gurbacewa a bangaren sufurin jiragen ruwa.
Taken bikin na bana na da alaka da muradan karnin majalisar dinkin duniya lamba na goma sha uku da na goma sha hudu na inganta teku, rafi da kuma muradi na goma sha bakwai wanda ya ke nuna muhimmancin hadin gwiwa da kuma aiwatar da muradun.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
Traditional institutions key to security, peace building in Nigeria, security – CAS
Air Chief tasks commanders to decisive airstrikes against bandits, terrorists
Tinubu Meets Senator Sani Musa, Commends Support for Reform Agenda
Datti Baba-Ahmed Defects to PRP, Picks Membership Card in Zaria
AI crucial for accountability in Nigerian varsities, says EFCC Chairman
National Development: Emir Sanusi urges universities to drive AI policy