Menu

Kiwon lafiya: Rashin katin Ganin likita ya sa marasa lafiya jin jugun jugun a asibitin yara na zoo road kano

Admin 4 years ago

Marasa lafiya sun shiga halin tsaka Mai wuya sakamakon karewar da katin da ake rubutawa marasa lafiya magani a cikinsa yayi, kuma wanda ke da alhakin ba da katin baya nan.

Wakilinmu da ya ziyarci asibitin yaga marasa lafiya sunyi jugun-jugun cikin takaicin rashin samun katin da zasu kaiwa likita don duba lafiyarsu.

Wani magidanci wanda ya kawo ‘yarsa jaririya wacce ka dama da zazzabi mai zafi ya koka bisa irin wannan halin ko in kula da wasu maaikatan asibitin ke nunawa kan lafiyar alumma, duk alkawarin da suka dauka kafin a basu aikin.

Akwai bukatar mahukunta suyi garanbawul kan irin wannan halin da maaikatan ke nunawa.