Majalisar wakilai ta Najeriya ta bayyana takaici tare da yin Allah wadai da kashe wata yarinya Ummukulsum Sani Buhari da wani Dan kasar Sin yayi a karshen makon daya gabata..
Majalisar tayi Allah wadai da lamarin ne Sakamakon kudirin gaggawa da Wakilin Kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure a majalisar Rt Hon Kabiru Alhassan Rurum yayi inda ya bayyana kisan a matsayin na zalinci Kuma Wanda ya Saba doka.
A yayin Dayake gabatar da kudirin Turakin na Rano ya bukaci majalisar ta yi Kira ga hukumomin tsaro su gudanar da kwakwkwaran bincike su Kuma gurfanar da Wanda ake zargin a gaban kotu Dan ya girbi abinda ya shuka.
Ya Kuma bukaci ‘Yan majalisar dasu tashi tsayi ayi shiru na Minti daya da zummar yin Addua ga marigayiyar tare da bukatar a kafa kwamitin da zai ziyarci Jihar Kanon da lamarin ya faru Dan jajantawa iyaye da ‘yan uwan Yarinyar dama Gwamnatin jihar baki daya..
Kudirin dai ya samu cikakken goyon baya ga daukacin ‘yan majalisar da suka halacci zaman in Banda wani Dan majalisar dake wakiltar wata mazaba a cikin Birnin Kano Wanda ya nuna rashin goyon bayansa tare da cewar Bai maga dalilin kawo wannan KUDIRI ba.
Tuni dai kudirin ya samu karbuwa Kuma majalisar ta amince da bukatu da Wakilin Kananan hukumomin na Rano, Kibiya da Bunkure Rt Hon Kabiru Alhassan Rurum ya gabatar cikin kudirin nasa…
A ranar Asabar data gabata ne dai wani Dan kasar China mazaunin Jihar Kano Geng Quarong ya haura har gidan su wata yarinya Budurwarsa Ummita dake Unguwar Jan bulo ya caccaka mata Wuka har ta mutu sakamakon kin karbar bukatar autensa da tayi..
Fatihu Yusuf Bichi
22/8/2022

Pantami Ta Tsaya Cak Yayin Da Dubban Jama’a Sukayi Tururuwar Tarbar Jamil Gwamna
AZMAN YA KADDAMAR DA SABON GIDAN SAI DA MAN FETUR NA ZAMANI A ABUJA, 28 ga Satumba, 2026
Naja’atu Muhammad; Pantami nada Suffar Munafikai
Zaben Gwamna A Gombe: Dalilan da Ya Sa Sardaunan Gombe Ya Zama Mafi Sauƙin Ɗan Takarar Gwamna da Za a Gabatar wa Jama’a
Amincin Tinubu Ga Barau Kan Harkar Tsaro Da Cigaban Kasa
Shugaban Ƙaramar Hukumar Kabo Hon. Lawan Najume Kabo ya sauke Sakataren Mulki na Karamar Hukumar da nadaddun Kansiloli huɗu, Saboda Shiga Ƙungiyar Tallata Shugaba Tinubu Da Sanata Barau (TMS) a Jihar Kano .
Nigeria, Russia Strengthen Customs Cooperation to Optimise Trade Facilitation, Information Exchange
NCoS Promotes 132 Officers in Kano, Controller Charges Beneficiaries on Professionalism
Senator Kawu Sumaila Commends Kano Drug Task Force, Donates ₦5m to Operatives, Supports Rescued Children
Nigeria’s Education System Needs Policy Consistency, Effective Implementation – Prof. Faruk Rashid Haruna
BPSR trains 660 federal officers on post-retirement productivity
Police Arrest Two Ekpo Masquerades Over Alleged Roadblock, Extortion in Akwa Ibom