Rundunar yan sanda ta Jihar Kano ta ce ta kama wani gungun masu ƙwacen waya su 6 da su ke addabar al’umma a jihar.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya baiyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi.
Ya ce an yi kamen ne bisa umarnin Sifeto-Janar na Ƴan Sanda kan cewa a tsaftace Kano daga duk wani aikin ɓatagari, musamman ƴan daba, ƴan ƙwaya da sauran laifuka, musamman a yayin bukukuwan Kirsimeti.
Kiyawa ya ce a na cikin sintirin ne a ka cafke waɗannan masu ƙwacen wayar su 6.
Ya ƙara da cewa an samu babura masu ƙafa uku da wayoyi 17 da su ka ƙwacewa mutane.
Kiyawa ya yi bayanin cewa masu laifin su na basaja ne a zuwan su matuƙa babur mai ƙafa uku ne sai su riƙa ƙwacewa fasinjoji wayoyin salula.
Ya ƙara da cewa idan an gama bincike, za ai kai su kotu domin su girbe abinda su ka shuka

Kaduna RAAMP Hosts Nasarawa Delegation on Study Tour
Rakibu Community Backs Rurum for Kano Deputy Governorship
Yusuf Clears N32bn Gratuities, Death Benefits Backlog in Kano
New Test Post 1
test34
test
Sharada Joins Kano Central Senatorial Race, Calls for Free and Fair APC Primaries
NEPC trains SMEs, MSMEs in Kano to boost export readiness
Traditional institutions key to security, peace building in Nigeria, security – CAS
Air Chief tasks commanders to decisive airstrikes against bandits, terrorists
Tinubu Meets Senator Sani Musa, Commends Support for Reform Agenda
Datti Baba-Ahmed Defects to PRP, Picks Membership Card in Zaria