Menu

Gwamna Bala Mohammad ya Nada Sabon Sarkin Ningi

Admin 2 years ago

Gwamnan Jihar Bauchi dake Najeriya Bala Muhammad ya nada Alhaji Haruna Yunusa Danyaya a matsayin sabon Sarkin Ningi domin gadon mahaifinsa Alhaji Inusa Danyaya da ya rasu a kwanakin baya.


Alhaji Haruna shi ne babban ‘dan marigayi sarkin kuma da wannan nadin ya zama Sarki na 17 a masarautar Ningi. Kafin wannan nadin, sabon Sarkin mai shekaru 68 ya rike sarautar Chiroma.

📷 Daily Trust