Rundunar ƴan sandan Jihar Kano ta jaddada cewar, har yanzu dokar hana goyo a babura masu ƙafa biyu ta na nan daram a jihar.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne, ya baiyana hakan a ranar Alhamis, bayan janye yajin aikin ƴan adaidaita-sahu da su ka yi na tsawon kwanaki uku.
Yajin aikin masu hayar keke Napep: Masu sana’ar Achaba na cin kasuwa a Kano
Time express Nigeria ta rawaito cewa, bayan da matuƙa baburan adaidaita-sahu su ka tafi yajin aiki a ranar Litinin, kwatsam sai a ka ga wasu na haya da baburan su, inda hakan ya fara firgita al’ummar jihar cewa ƴan Achaba za su dawo.
Da ya ke zantawa da manema labarai, DSP Kiyawa ya ce dokar hana goyo a babur, wacce gwamnatin jihar ta kafa a 2013, tana nan daram.
Ya ce, “Rundunar ‘yan sanda ta baza jami’anta, domin tabbatar da dokar, saboda haka al’umma su kiyaye.”

Kaduna RAAMP Hosts Nasarawa Delegation on Study Tour
Rakibu Community Backs Rurum for Kano Deputy Governorship
Yusuf Clears N32bn Gratuities, Death Benefits Backlog in Kano
New Test Post 1
test34
test
Tinubu Meets Senator Sani Musa, Commends Support for Reform Agenda
Datti Baba-Ahmed Defects to PRP, Picks Membership Card in Zaria
AI crucial for accountability in Nigerian varsities, says EFCC Chairman
National Development: Emir Sanusi urges universities to drive AI policy
Group Endorses Senator Barau for 2027, Cites Development Record in Kano North
How AA Zaura escaped mob attack by miscreant at Farm centre