Menu

GIDAN RADIO NAJERIYA NA KADUNA RUMBU NE WAJEN ADANA TARIHI DA AL’ADUN AREWA DAMA KASA BAKI DAYA – SARKIN KANO.

Admin 4 years ago

anbayyana gidan radio tarayyana na kaduna amatsayin wurinda ya dade yana adana Al’adun arewa da tarihi na tsawon lokaci akasar nan.

Bayanin hakan yafito ne daga bakin Mai martaba Sarkin kano Alh, Aminu Ado Bayaro, awata zantawa da wakilin gidan radion ranar laraba kan batun chikar gidan rediyon shekaru 60 da kafuwa.

Mai martaba Sarkin kano yakuma Kara dacewa lallai za’a kwashe shekaru ana amfana da ayukan wannan tasha mai tarin albarka da amfanar da jama’a.

Sarkin yaciga da bayyana tashar rediyon tarayya na kaduna babu shakka yakasance wani jigo na hada kan al’ummar kasar musamman lokutan da akayi yakin basasa da wasu rikice-rikice dasuka faru.

Sannan yajadda cewa wannan kafa yada labaran yadade yana fadakar da jama’a hadi da ilimantarwa akasar na tsawon shekaru sittin dasuka fara gabatarda shirya-shiryensu.

Aminu Ado ya kuma bukaci gwamnati data shigo ciki wajen samar ma da wannan kafa kayan aiki na zamani da inganta walwalar ma’aikatan dake aiki agidan dan daukaka matsayin kasar nan.

Sarkin yace lallai tun tasowarsu basu san wani gidan radio kamarsa ba wajen fadakar da al’umma, dan Kuma su kansu sun samu riba wajen sauraren wannan gidan radio da bada bada sahihan labarai da duk wanda yake kasar nan bama arewaba kadai.

Sannan yakara tabbatar dacewa wannan gidan radio yafi dukkan wasu kafofin sadarwa nazamani muddun akasamo hanyar da za’a inganta rayuwar matasa da tsamosu daga matsalar dake faruwa ahalin yanzu da dayawan matasa suna fadawa ciki.

Daga karshe mai martabar ya bayyana taya ma’aikatan gidan radio murna bisa yadda suke gabatar da shirya-shiryensu atsawon shekaru 60 dafara aikin su.