Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP tare da komawa jam’iyyar APC.
Mbah ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a Enugu, inda ya ce matakin nasa na komawa APC ya biyo bayan burinsa na inganta hidima ga al’ummar jihar da kuma daidaita kansa da hangen nesa na jam’iyyar wajen ci gaba da bunƙasa tattalin arziki.
A cewarsa, shiga jam’iyyar APC zai ba da dama mafi faɗi na haɗin gwiwa da ci gaba da zai taimaka wajen bunƙasa Jihar Enugu.
“Na kuduri aniyar ci gaba da inganta cigaban jiharmu tare da tabbatar da cewa jama’armu suna amfana da mulkin da ya dogara da haɗin kai da ci gaba mai ɗorewa. Tsarin jam’iyyar APC zai ba mu damar cimma waɗannan manufofi,” in ji shi.
Gwamnan ya kuma bayyana godiya ga tsohuwar jam’iyyarsa, PDP, bisa goyon baya da ta ba shi tsawon shekaru, yana mai cewa matakin sauya sheƙa ba abu ne da aka ɗauka da wasa ba.
Asalin Labari…. Daily Nigeria Hausa

Naja’atu Muhammad; Pantami nada Suffar Munafikai
Zaben Gwamna A Gombe: Dalilan da Ya Sa Sardaunan Gombe Ya Zama Mafi Sauƙin Ɗan Takarar Gwamna da Za a Gabatar wa Jama’a
Amincin Tinubu Ga Barau Kan Harkar Tsaro Da Cigaban Kasa
Shugaban Ƙaramar Hukumar Kabo Hon. Lawan Najume Kabo ya sauke Sakataren Mulki na Karamar Hukumar da nadaddun Kansiloli huɗu, Saboda Shiga Ƙungiyar Tallata Shugaba Tinubu Da Sanata Barau (TMS) a Jihar Kano .
Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
Kano Govt Empowers 5,800 Women With N290m Grants
H E DR Amina Umar Namadi Receives Outpouring of Love, Goodwill from Well-Wishers
Kano Govt Condemns Attack on Journalists, Demands Justice
WHY PANTAMI SHOULD NOT BE TRUSTED WITH THE GOVERNANCE OF GOMBE: 2027
City Boy Movement Targets 10m Votes for Tinubu in 2027
MUHAMMAD GARBA Redeems Pledge, Donates Smart TV to Kano Correspondents’ Chapel