Menu

Mu hada hannu wajen kula da ilmin ‘ya ‘yanmu -MARAFAN MADAKIN KANO

Admin 4 years ago

An kira da iyaye su kara dagewa wajan Taimakawa Makarantun islamiyyu da na Karatun Allo don cigaban ilmi baki daya.
Wannan kira ya futo data Marafan Madakin Kano a wajan Saukar Karatun Al’kur’ani na Dalibai guda (20) a makarantar koyan Addini da Ilimin Al’alku’ani ta Unguwar Diso, dake karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano.
Alhaji Bashir Idris Diso ya yi dogon Bayani akan Hakkin Iyaye akan Yayansu da kuma Hakkin Yaya akan iyayensu.

Mai girma marafan madakin kanon ya kara da yabawa Malaman makarantun Islamiyyoyi da makarantun Allo, yada suke kokari wajan zaburar da Dalibai gun Illimin Addini,Ya kuma kira da masu Hali dasu dinga Tallafawa irin Wadannan makarantun da kayan Karatun,abubuwan zama, da Shawarwari Dan ganin an samu Nasarori wajan gudanar da karatuttuka a makarantun. 
Shima a Nashi Jawabin Shugaban Makarantar Alh. Shu’aibu Mas’ud ya godewa malaman makarantar bisa kokarinsu da kuma Sha’awarsu wajan ganin makarantar ta ci gaba. 
Shima a mashi jawabin Mai’unguwar Diso, Alh. Ahmad Bello Diso, ya godewa Matasan da ke yankin bisa kokarinsu na naiman ilimi da kuma kauracewa Rudin Duniya da sauran Futunu a yankin. Haka kuma, wani Dattijo Alh. Abdulkadir Hassan ya godewa daukacin Mahaddatan, tare da fatan su kara dagewa wajan tulawa da sauran  karatattukansu Littattafan Addini.