Naji dadi matuka wajen ganin na shiga jerin mutanan da suke maka fatan alkairi da turo sakon taya murna akan zamanka a matsayin sabon shugaban jamiyyar APC na kasa. A matsayin ka na sabon shugaban babbar jamiyya a nahiyar afrika gaba daya. Abubuwan da suke gaban ka a bayyane suke amma abinda zakayi akan su bazai wuce ka nemi taimakon Allah ba tare da adduar ganin shugabancin ka ya kawo daidaito da hadin kai da muka dade muna fata domin ganin mun cika alkawarutukan da muka yiwa alumma.
Ina ganin kaina a matsayin me babbar saa a wannan kadami, saboda na sanka kuma na hadu da kai tare da yin muamala a lokacin da nake tasowa. Saboda haka na san kai mutum ne me gaskiya tare da gogewa a shaanin mulki musamman jagorantar alummar data kunshi mutane masu aladu da addinai daban daban.
Wannan salo naka na ganin ka samawa alumma hadin kai shine yasa ake kallon ka a matsayin wani mudubi wanda a karshe aka saka maka suna a matsayin ‘The Bridge’ wato ‘Gada’ wacca take hada alumma daban daban.
Ba wata muamala da nayi dakai a baya da kuma yanzu da bai zamo wani alamari da ya kara min kwarin gwiwa ba amma ba kayi kasa a gwiwa ba wajen ganin ka zaunar damu domin bamu labarin gogewar ka wacca zata daura mu akan irin wannan hanya.
Daya daga cikin darassukan dana samu shine zamana mamba a kwamitin da ya tayaka yakin neman takara shugaban kasa shekaru sha shida da suka wuce. Wannan kuma ya samu asaline wajen ganin kayi jagoranci da zai banbanta dana baya a wannan kasa Najeriya.
Nine nafi kowa karancin shekaru a cikin wannan kwamitin dake nema maka shugabancin kasar nan amma ka dage kwarai da gaske wajen ganin na halarci duk wani taro a wannan lokacin, mun zaga cikin wannan kasa mun shiga kasuwanni domin ganin mafarkin ka na kawo cigaba ya tabbata.
Na karu matuka kuma wannan ne ya bani damar da ka tabbatar min cewa ka yarda matasa sunada rawar da zasu taka a wannan kasa da kuma fadin ka na cewa matasa sunada duk wani abinda ake nema na kawo wa kasa cigaba.
Na kara samun damar haduwa dakai a majalisa ta 7, 8 da kuma ta 9. Abin mamaki da almara shine yanda muna daga cikin shugabannin da suka tabbatar da ficewar kaso 80 na yan majalisun tarayya da Sanatoci daga jamiyyar PDP zuwa APC a lokacin muna tunkarar zabe a shekarar 2015.
Wannan wani juyi ne da kuma rawa wacca muka taka wacca ba a taba samun irin ta ba a wannan kasa.
Sannan a majalisa ta 8 kaine shugaban yan majalisu da sanatoci masu goyon bayan shugaba Buhari a zauren majalisar dattijai ni kuma nine na majalisar wakilai. Wannan shine ya bamu dama wajen ganin mun hada kan yan majalisu domin marawa shugaban kasa baya a karkashin jagorancin ka mun yi kokari sosai wajen ganin yan majalisun mu da suke a jamiyyar APC basu sauka daga layi ba wajen ganin an zabi shugabannin da jamiyya ta gindaya su zama shugabannin majalisar dattijai data wakilai.
Ya ne girma Shugaba, wannan kadan daga cikin tarihin siyasata da kaine kuma tabbas ka cancanta daka zama shugaban jamiyyar APC duba da gwagwarmayar da kayi mata.
Kwarraren Injiniya, lawyer, tsohon shugaban NTA da kamfanin simintin Benue, mamba a majalisar kasa da kuma taron gyaran kundin tsarin mulki(1979, 1994) Minista, Gwamna, Sanata kuma sanannan manomi, bazan iya cigaba da kawo su ba domin suna da yawa. Takaradun karatun ka tabbas da sauran nasarorinka sune suka sama maka sarautar gargajiya ta Sarkin Yakin Keffi da kuma Turakin Keffi a yanzu saboda kaunar ka da sarautar gargajiya.
Nasan ka kwatai da gaske kuma zan bada shedar nagartarka, darajarka da kuma yanda kake kallon matsaloli, tabbas kai mutum ne me ganin a ko yaushe an warware matsala. Ba abin mamaki bane a tsawon shekaru 40 kana siyasa baka taba rashin nasara a zabe ba.
A saukake zan iya cewa yanzu APC tana hannun da ya dace, tabbas zakayi amfani da ilimin ka da gogewar ka wajen ganin ka ciyar da jamiyyar mu gaba tare da samun nasara.
Ina tayaka murna sosai, Allah ya tayaka riko. Ameen.
Danka, Abdulmumin Jibrin
1/4/2022

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
Sharada Joins Kano Central Senatorial Race, Calls for Free and Fair APC Primaries
NEPC trains SMEs, MSMEs in Kano to boost export readiness
Traditional institutions key to security, peace building in Nigeria, security – CAS
Air Chief tasks commanders to decisive airstrikes against bandits, terrorists
Tinubu Meets Senator Sani Musa, Commends Support for Reform Agenda
Datti Baba-Ahmed Defects to PRP, Picks Membership Card in Zaria