Har yanzu bai bayyana aniyarsa ba
za a ji matsayata nan ba da jimawa ba-Jamoh
Shugaban Hukumar Kula da sufurin Jiragen Ruwa ta Najeriya, NIMASA, Dr. Bashir Yusuf Jamoh ya fara tuntuba game da aniyarsa na neman takarar gwamna a daidai lokacin da wa’adin murabus din duk wasu masu rike da mukaman siyasa ke kara matsowa.
Jamoh wanda ya fara neman tabarraki daga gidansa da al’ummarsa da kuma masarautar Zazzau, ya ce matakin na daga cikin irin tarbiya da ya samu daga gida na neman albarkar dattijai da abokan arziki da sauran Yan Uwa da abokan arziki kafin ya fara duk wani muhimmin aiki da ya tasa baba.

Da yake jawabi a wajen wani taro a unguwarsu dake anguwar juma a cikin birnin Zariya, babban daraktan ya sanar da su a hukumance irin buri da muradin jama’a na ganin ya dawo jiharsa domin yi wa al’umma hidima.
Jamoh wanda ya samu tarba daga Wazirin kuma Babban Limamin Zazzau, Khadi Mohammed Aminu da Sheik Dalhat Kasim, ya samu karramawa da yabo bisa irin nasarorin da ya samu a NIMASA.
Daga nan sai ya ziyarci mai martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli domin samun albarkar masarautar.

Da yake jawabi jim kadan bayan ziyarar, Dr.Jamoh ya shaidawa manema labarai cewa har yanzu bai bayyana matsayarsa ba na tsayawa takarar gwamna a hukumance ba har sai an kammala tuntubar tukuna.
“Na zo nan ne domin in tuntubi ‘yan uwana, da alummar gari da kuma majalisar masarautara Zazzau kafin in dauki wani mataki kan lamarin.
“Ina sane da cewa mutane sun yi ta sanya fosta na a duk fadin jihar amma ina so in sanar da ku cewa ban sanya wani ya sanya ko daukar nauyin wannan yunkuri ba.
“Duk sun yi hakan ne saboda kauna da kuma matsa min na mika wuya ga burinsu da Kuma na yi alkawari zan bayyana matsayina cikin kankanin lokaci.
“Abin da nake bukata a wurin mutane yanzu shi ne addu’ar neman zabin Allah a kan dukkan abin da muke yi.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
Traditional institutions key to security, peace building in Nigeria, security – CAS
Air Chief tasks commanders to decisive airstrikes against bandits, terrorists
Tinubu Meets Senator Sani Musa, Commends Support for Reform Agenda
Datti Baba-Ahmed Defects to PRP, Picks Membership Card in Zaria
AI crucial for accountability in Nigerian varsities, says EFCC Chairman
National Development: Emir Sanusi urges universities to drive AI policy