Shugaban hukumar kula da kare kan iyakokin ruwa na kasa, Dr Bashir Jamoh ya bada tabbacin samar da jirage biyu na musamman a wani mataki don yakar satar mai da kuma tsare tattalin arzikin kasa.
A wata sanarwa da mataimakin darakta a sashin hulda da jama’a na hukumar, Mr Osagie Edward ya fitar yace shugaban hukumar ya bada wannan tabbacin ne a wurin taron karawa juna sani a bangaren harkokin iyakokin ruwa da aka shiryawa alkalai karo na goma sha shida wanda majalisar fito ta kasa ta shirya, Dr Bashir Jamoh ya bayyana satar mai, barnata bututun mai da kuma tace mai ba bisa ka’ida ba a matsayin ababen da suka sabawa dokar kasa wanda ya kan iya yin barazana ga tattalin arziki, muhalli da jin dadin al’ummar kasar nan.
Yace jiragen wadanda na tafi da gidanka ne, zasu taimakawa sauran jiragen da sauran hukumomin tsaro suka tanada wadanda hukumar NIMASA take da yarjejeniya ta fahimta tsakanin ta da su.
Jamoh yayi bayanin cewa jiragen za su taimaka wajen yin sintiri akan gine-ginen gidajen man fetur da kuma sauran kadarorin kasa don bankado take-taken mabarnata da masu kai hare-hare ga jiragen ruwan dake yawo a bangaren da gine-ginen man suke.

Da yake jaddada aniyar hukumar wajen kare iyakokin ruwan kasar nan kuwa, Dr Bashir Jamoh ya tunatar da mahalarta taron akan kudirin Shugaba Muhammadu Buhari wajen karfafa gwiwar masu ruwa da tsaki da masu zuba hannayen jari a bangaren bangaren iyakokin ruwan kasar nan.
A cewar shi, amincewar shugaban kasa don sayo jiragen da kuma zuwan da yayi don kaddamar su a ikko da kuma amfani da su don aikin tsaro sun taimaka matuqa wajen yaki da laifuffuka akan iyakokin ruwan kasar nan.
Yace hukumar za ta tayi amfani da jiragen biyu na musamman don lura da kuma yaki da satar mai a kasar nan. Da wannan, hukumar na nufin amfani da jiragen don yin sintiri a muhimman wurare don sa ido akan miyagu da kuma lura da zirga-zirgar jiragen ruwa da samun bayanan sirri akan lokaci da zai ba hukumomin tsaron mu damar daukar matakan da suka dace.
“Bangaren man fetur na da tasiri ga tattalin arzikin kasa kuma bai dace a ba miyagu daman mamaye bangaren ba. Muna da bayanan nasarorin da hukumomin tsaron kasar suka samu wajen kare kan iyakokin ruwan kasar nan, amma sai an kara bada himma don dorewar wadannan nasarorin.
“Kadan daga cikin hadin gwiwa da yarjejeniyoyin mu da hukumomin tsaro sun hada da aiki tare don dakile ayyukan miyagu kafin su farga. Ina mai farin ciki ganin yanda hadin gwiwar mu ya amfani kasar nan ta fuskoki da dama a cewar Dr Bashir Jamoh.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
Former Kano Federal Lawmaker Shaaban Sharada Distances Self From Barau Group’s Endorsement of New Deputy Governor
K-SAFE Hails Gov Yusuf Over ₦4.45bn Approval for Students’ Examination Fees
Governor Radda Inaugurates 2026 Hajj Committee, Charges Members on Integrity
Kenyan President Calls For Radical Overhaul Of African Union
Police Commissioner Visits Mada, Meets Stakeholders Over Rising Security Concerns in Zamfara
MALNUTRITION: Governor Radda Opens 2 Stabilization Centres, 60 OTP Sites,