Menu

DAG DA ACTION AIDS SUN SHIRYA TARON BITA KAN TSARO DA WANZAR DA ZAMAN LAFIYA A JIHAR KANO.

Admin 4 years ago

BABANGIDA SANUSI KANO.

Kungiyar wanzar da damokuradiyya ta kasa hadin gwuiwa da kungiyar jinkai da tallafawa marassa galihu da kokarin rage talauci ta duniya sungudanar da taron wayarma da al’umma kai wajen mahimmancin hadin Kai da samar da tsaro karkashin kwamitin sa’ido kan harkar tsaro da daidaiton al’umma awasu kananan hukumomin jihar kano.

Da yake jawabi yayin taron shugaban kungiyar ta samar da zaman Lafiya da wanzar da damokuradiyya DR.Muhammad Mustapha yace yunqurin su shine suga jama’a na maida hankali wajen taimakon jami’an tsaro wajen kula da yankunan da suke zaune dan tabbatar da waye,menene tareda dalilan faruwar matsalolin dan daukar matakin daya dace na hukunci.

Dr Mustapha yacigaba dacewa bukatarsu anan itace duk wanda yazo wannan taro matsayin sa na memba ya koma garinsu da unguwar su dan wayarma da sauran jama’a kai na magance abubuwan da ka iya bijirowa na rikice-rikicen zasu kai matsayin fin karfin mutane da jami’an tsaron ma kansu.

Shugaban yakara dacewa dokar kasa taba kowane d a dan kasa damar kama Mai laifi tareda mikama jami’an tsaro dan daukar mataki batare da daukar mataki da kansu ba,shine wannan aikin su wadanda suka zabo daga kowace qaramar hukumar da kuma mazabu biyu a qananan hukumomi takwas na jihar kano.

Sannan yace suna kokarin ba wadanda suke cikin wannan kwamitin bitar yanda zasu sassanta karamar matsalar da zata iya bijirowa acikin anguwanninsu hadi da sanar da irin abubuwan dake zuwa da dawowa na sa ido magancewa batare zuwa ko ina ba ta hanyar sulhu.

Shima anasa jawabin tun farko mataimakin daraktan kungiyar action aids na kasa Mr Anicetus, yace lallai aduk matsalolin dake faruwa a yankunan mu nadaga rashin zaman lafiya akwai masaniyar mazauna yankin.

Mr Anicetus yana mai tabbatar da cewa dalilin zaqulo wadannan mutane shine dan nusar dasu hanyoyin da zasubi dan wanzar da zaman lafiya acikin al’ummar su dakuma sasanta matsalolin gurarensu,inda kuma yace bayan wannan kuma zaau tabbatar da haxa wadannan Yan kwamitin da sauran masu riqe sarautun gargajiya.

Shima jami’in gudanar da shirye shirye na kungiyar wanzar da zaman lafiya Abdulbaqi Muhammad Yusuf yace bukata anan shine kowa yazama mai kula da abinda kefaruwa ayankunan su.

Sannan Abdulbaqi Muhammad yabayyana jin dadinsa na yadda mutane suka fara fahimtar yadda zasu sanar da hukuma misali a tudun wadar dankade da masu sana’ar acava dasuke taron wayar da Kan junansu gameda sana’ar su kan mutanen dasuke xauka musamman baki.

Abdulbaqi yakuma bukaci mahalarta bitar dasu zama jakadu nagari tareda sanar da hukuma mafi kusa tundaga matakin mai unguwa har jami’an tsaron civil defence, Yan sanda hukumar kare haddura da sauran vangarori na tsaro dan daukar mataki.

Wasu daga cikin wadanda ake ba bitar daga kananun hukumomin Bichi da Gwarzo sunbayana samun cikakken kwarin guiwa da kuma dabarun yadda ya kamata su sanar da duk wani motsi da basu ganeba ayankunan su tareda taimaikon juna wajen dogaro da kawunansu.

Taron wanda yagudana a dakin taro na tahir guests palace dake karamar hukumar Nasarawar jihar kano yasamu halartar shugabanin kwamitin na Cart tareda membobinsu daga kananan hukumomin Bichi,Gwarzo,Gwale, Nasarawa tudun Wada, Bebeji, da aka dauki garuruwa biyu daga kowace karamar hukuma.