Gidauniyar dag datake gudanar da aikinta karkashin uwar kungiyar ta kasa watau action aid tabi sauran kungiyoyin duniya wajen gudanar da taro kan hanyoyin da matasa zasu bi dan samun hanyoyin dazasu zama mafita arayuwarka ta yau da kullum.
Datake jawabi yayin taron daraktar gidauniyar ta kasa mrs,Ene Obi, tayi matukar farin ciki da irin yadda al’umma jihar kano suke ba wannan kungiya goyon baya tareda da hadin kai daya samo asali wajen jajircewar shugaban wannan gidauniya da sauran ma’aikatan ta na jihar wajen shiga lungu da sako na Kano dan yada manufar wannan kungiya.
Sannan Mrs Ene Obi tace a najeriya jihar kano nada mutane kashi 59.43 bisa dari dabasu da aikin yi a kwata ta biyu a wannan shekara ta 2022 da yake babban kalubalene ga Al’ummar mu da mu kanmu da zai iya kawo matsalar rashin zaman Lafiya.
Sai dai Kuma Ene Obi tasanar cewa abin Alfahari ayanzu shine ayunkurin da wannan gidauniya take da sauran kungiyoyin duniya yasa matasa nakara fahimtar suwaye su da kuma hanyoyin dazasu taimaki kansu ko dogaro da Kai.
Shima anasa jawabin mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayaro daya samu wakilcin Dan majen Kano yayin gudanar da taron na ranar matasan ta duniya yafara godiya ga wannan gidauniya ta action aids bisa kokarinsu na samama matasa hanyoyin dogaro dakai da kaucewa abin da yake kawomana tashin hankali ahalin yanzu.
Sarkin yakuma shawarci matasan dasu zama masu neman nakansu dazai iya magance matsalar da akafi kallonsu da ita ta shaye-shaye harkar daba dakuma bangar siyasa harma da harkokin garkuwa da mutane dan kudin fansa da ayanzu yazama ruwan dare a najeriya.
Kazalika Mai martaba yakuma bukaci kungiyar ta action aids takara fadada ayukanta zuwa dukkan Kananan hukumomin jihar kano dan cigaba da wayarma jama’a Kai da fahimtar dasu hanyar dazasu bi dan kaucewa hargitsi da cece kuce, yayin da Kuma yakara bukatar cigaba da shiga jaridu da radio talabijin dan kara wayarma da al’umma Kai.
Shima anasa jawabin tunfarko shugaban tafiyar na jihar kano Alhaji Dr.Muhammad Mustapha yayi matukar godiya ga Allah daya basu damar gudanar da wannan taro a Kuma wannan rana ta matasa da majalisar dinkin duniya ta fidda dan zama da jin irin cigaba da matsalolin da matasa suke samu tareda samo hanyoyin magance su.
Sannan Dakta Muhammad Mustapha yace kokarin su shine koda yaushe mata da matasa suzama kangaba wajen tafiyar da harkokin rayuwa tareda sannin illolin da sukan iya fadawa yayin gudanar da wasu ayukan dana sani dazai iya sa su cikin kunci na rayuwa.
Cikin wadanda suka samu halartar taron akwai Wakilan gwamnati, jami’an tsaro da masu rike da sarautun gargajiya da masu ruwa da tsaki da dai sauran al’umma daban.
Taron dai yagudana a dakin taro na “The avenue event center”dake kusa da asibitin karamar hukumar nasarawar jihar kano.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
Traditional institutions key to security, peace building in Nigeria, security – CAS
Air Chief tasks commanders to decisive airstrikes against bandits, terrorists
Tinubu Meets Senator Sani Musa, Commends Support for Reform Agenda
Datti Baba-Ahmed Defects to PRP, Picks Membership Card in Zaria
AI crucial for accountability in Nigerian varsities, says EFCC Chairman
National Development: Emir Sanusi urges universities to drive AI policy