Menu

HUKUMAR NIMASA TAYI GARAMBAWUL A KUDADEN TALLAFIN HORAS DA MA’AIKATAN TA.

Admin 4 years ago

Hukumar kula da iyakokin ruwan kasar nan-NIMASA a halin yanzu tana bitar kudaden tallafin karatu da take kashewa ga daliban kasar nan dake karatu a kasashen ketare a karkashin shirin inganta sufurin jiragen ruwa.

A sanarwar da mataimakin darakta a sashin hulda da jama’a na hukumar Mr Osagie Edward ya rabawa manema labarai yace Shugaban hukumar ya lura da cewa yin garambawul din ya zama tilas bisa la’akari da tabarbarewwar tattalin arzikin duniya musamman ma a kasar Philippines, India da sauran kasashen da daliban Nijeriya ke karatu.

Ya kara da cewa duk da yake NIMASA ta biya dukkan kudaden da suka shafi kudin makaranta, na jarrabawa da kuma alawus ga daliban, rayuwa tayi tsada a kasar Philippines, inda yayi nuni da cewa hukumar na aiki da ofishin jakadancin Nijeriya dake kasar ta Philippines kan hanyoyin da za a bi wajen tunkarar wannan kalubalen na tsadar rayuwa a kasar.

Dr Bashir Jamoh yace hukumar ta yi shirye-shirye na gajere da dogon zango don rage kaifin tasirin sauyin da aka samu inda hukumar ta amince da karin dala dubu biyu ga duk dalibi.

Yace dalibai dari da arba’in da shida sun samu lasisin tukin jirgin ruwa yayin da wasu dari da talatin da hudu na kan yin karatun neman lasisin, sannan kuma wasu dari da saba’in na shirin tafiya zuwa kasar ta Philippines don yin nasu jarrabawar.

A shekarar 2008 ne hukumar ta samar da shirin inganta sufurin jiragen ruwa saboda karancin yan kasa a sha’anin sufurin jiragen ruwa da kuma horas da matasan kasar nan a kwararrun cibiyoyin horas da ma’aikatan jiragen ruwa.

Tun kafuwar wannan shirin, hukumar ta horas da dalibai kimanin dubu biyu da dari biyu da arba’in da daya inda dari takwas da arba’in da daya daga cikin su sun samu nasarar samun lasisin tukin jiragen ruwa daga kasashe daban-daban.

Har ila yau, dari uku da tamanin da takwas sun samu ayyukan yi a ma’aikatun kula da iyakokin ruwa daban-daban, yayin da kuma sauran na matakin karshe na karatun su.