Menu

SHUGABAN HUKUMAR NIMASA YA ZIYARCI SHEDIKWATAR TSARO NA KASA

Admin 4 years ago

Shugaban hukumar kula da iyakokin ruwan kasar nan Dakta Bashir Yusuf Jamoh yace wajibi the hukumar ta cigaba da hadin gwiwa tsakanin ta hukumomin tsaron kasar nan da kare martabar iyakokin ruwan kasar nan.

Dakta Bashir Yusuf Jamoh ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci shedikwatar rundunar tsaron kasar nan dake Abuja.

Shugaban hukumar yace hadin gwiwar da hukumar tayi da wasu hukumomin tsaro a baya bayan nan ya taimaka matuqa wajen rage aukuwar manyan laifuka akan iyakokin ruwan kasar nan.

Dr Bashir Jamoh yace hukumomin tsaro sun bada gagarumar gudunmawa wajen bada tsaro ga jiragen dako na ruwa a iyakokin ruwan kasar da kuma na tafkin guinea.