Daga Abdullahi Kano
Dan Takarar mataimakin Gwamna Karkashin Tutar Jam’iyyar APC a kakar Zabe Mai Zuwa Alhaji Murtala Sule Garo ya ce Idan Allah ya Lamunce Aka Zabe su,a zaben gwamnan da ke tafe to za su dora ne akan ayyukan raya kasan da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya faro.
Alhaji Murtala Sule Garo ya Bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a kano.
Yace Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi matukar kokari ta fannin sauya rayuwar alummar jihar kano, kuma in har alummar kano suka bamu dama ta hanyar zaben mu to babu shakka ba zamu basu kunya ba.
Murtala Garo ya kara da cewar bunkasa cigaban ilmi, lafiya, noma ta tallafawa matasa don su zamo masu dogaro da kawunansu na data cikin bangarorin da zamu fi baiwa fifiko.
“Babban abin da zamu sa a gaba in Allah ya bamu nasara shi ne inganta rayuwar alummar mu”
Sanin kowa ne gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bullo da shirin nan na ba da ilmi kyauta kuma dole, babu shakka geamnatinmu za ta dora akan hakan in Allah ya bamu nasara.
Munyi tsarin samar da ingatattun dakunan shan magani a dukkan mazabu 484 da ke fad in jihar kano.
Dan takarar mataimakin gwamnan yace sun kuma yi shirin kawo sabbin na’urorin noma na zamani don tallafawa manoma, wanda hakan zai kara bunkasa samar da abinci da karin guraben ayyukanyi a jihar kano.
Garo ya kuma ba da tabbacin cigaba da yin tituna a yankunan karkara da birni don saukakawa manoma fito da amfanin gona zuwa kasuwanni, wanda hakan zai kara Habaka tattalin arzikin jihar.
” ba zamu yi kasa a gwiwa ba wajen baiwa matasa jari tare da koyar da su sanaoin dogaro da Kai, don su dogara da kansu, harma su dauki wasu aiki”

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
After Intense Meetings: Kano APC Stakeholders Nominate Sule Garo As Deputy Governor
APC Legacy Stakeholders Submit Deputy Governorship Nominees to Gov. Yusif
Yusuf Disburses N50,000 Monthly Support to 6,680 Women Across Kano
NSCDC Kano Command Tests Surveillance Drone to Boost Security Operations
Police Raid Criminal Hideout, Arrest Suspects, Recover Firearm, Illicit Substances in Akwa Ibom
CP Bello Inspects Police Constables Screening Exercise in Gusau