Hukumar kula da iyakokin ruwan kasar nan wato NIMASA tace tana nazarin faifan bidiyon dake yawo a shafukan sada zumunta na zamani dake nuna yanda wasu dalibai sukayi zanga-zanga a ofishin jakadancin Nijeriya dake kasar Philippines.
A wata sanarwar da ta samu sa hannun mataimakin darakta a sashin hulda da jama’a na NIMASA, Mr Edward Osagie, kuma aka rabawa manema labarai, yace hukumar ta samu sahalewar ma’aikatar sufuri don ziyarar gani da ido zuwa Philippines da zimmar gano musabbabin zanga-zangar, don gano bakin zaren.
Sanarwar tayi bayanin cewa Babban Darakta mai kula da hada-hadar sufurin jiragen ruwa a hukumar, Injiniya Victor Ochei ne ake sa ran zai jagoranci ziyarar zuwa kasar ta Philippines don gano hanyar warware matsalar cikin ruwan sanyi.
Sanarwar tayi Allah wadai da wannan abin kunya da wadancan dalibai su kayi, sannan hukumar ta bukaci jama’a da su guji yada jita-jita har sai an gano musabbabin zanga-zangar.
Ana sa ran gabatar da rahoto a hukumance daga NIMASA da zarar an kammala ziyarar aikin gani da idon.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
Arrest of Bello Bodejo politically motivated – Campaign DG
Police Violent Crime Response Unit Records Breakthrough in Akwa Ibom Raid
2027: Church Urges Effective Deployment of Technology, Establishment of Election Offense Commission
Police, Military Recover 67 Stolen Cows, Other Livestock in Kano
Former Presidential Aide, Ja’oji, Gets House of Reps Ticket
Zamfara Police Commissioner Holds Strategic Security Meeting with Senior Officers