Shugabannin kungiyar kwararru masu hada-hadar sufuri ta kasa ta sanar da dakatar da zaben da tayi shirin gudanarwa.
Shugaban kwamitin zabe na kungiyar, Farfesa Innocent Ogwude ne ya shaidawa manema labarai hakan a Abuja.
A cewar shi, Shugaban kungiyar Dr Bashir Jamoh da kuma sakataren kungiyar ta kasa Mr Chinda Evans Ogbuji sun sanya hannu a taron gaggawa na majalisar zartaswan kungiyar, inda suka bayyana cewa dakatar zaben yayi daidai da tsarin dokokin kungiyar.
Yace majalisar zartaswan ta dakatar da zaben ne don sake tsare-tsaren gudanar da sahihin zaben da zai samar da sabbin shugabannin kungiyar.
Dr Bashir Yusuf Jamoh yayi kira da kwamitin zaben da su guji son rai, kuma kada su yarda wani ya tilastasu wurin yin ba daidai ba, wanda a cewar shi, yin haka zai zubar da kimar kungiyar a idon jama’a.
Ya kuma jaddada aniyar kungiyar na baiwa ko wane dan takara dama, ba tare da tsangwama ba, inda yayi nuni da cewa kungiyar ba za ta lamunci karya dokokin da ke kunshe a tsarin dokar kungiyar ba.
Ita dai wannan kwamitin zabe dake karkashin Farfesa Innocent Ogwude na da alhakin gudanar da zabe ne a taron shekara-shekara na kungiyar da aka sa ran yi a karshen makon watan Nuwamba mai zuwa.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
CP Azare Commends Peaceful Conduct of APC Primaries in Akwa Ibom
Kano South Fallout: Has Rurum Drawn a Red Line Against Kawu Sumaila?
When Ja’o’ji Answers Reconciliation With Humility in Victory
APC Aspirant Raises Concerns Over Conduct of Primary Election in Jigawa Constituency
Kano Govt Pledges Stronger Collaboration with FG, Partners on Education
Ambassador Dr Amina Umar Namadi Sponsors Mass Marriage for 300 Couples in Jigawa