An yabawa Shugaban hukumar kula da iyakokin ruwan kasar nan Dr Bashir Yusuf Jamoh dangane da gudunmawar da yake badawa wajen ciyar da bangaren sufurin kasar nan gaba.
A sanarwar da mataimakin darakta a sashin hulda da jama’a na hukumar NIMASA Mr Edward Osagie ya rabawa manema labarai a jihar Legas ya ce Shugaban ya samu yabon ne a wajen taron karawa juna sani na kasa karo na hudu wanda cibiyar kula da zirga-zirga ta kasa ta shirya a birnin tarayya.
A wani labarin na daban kuwa, rundunar sojin kasar nan da sauran hukumomin tsaro sun bada tabbacin bada goyon baya wajen inganta bangaren sufurin kasar nan, da kuma hada hannu da cibiyar kula da zirga-zirga ta kasar nan.
READ ALSO:BABBAN SAKATAREN KULA DA IYAKOKIN RUWA NA DUNIYA YA KADDAMAR DA SABON GININ SHEDIKWATAR NIMASA
Babban hafsan rundunar, Laftanar Janar Faruk Yahaya ya bayyana hakan ta bakin Manjo Janar E Akerejola inda ya yabawa cibiyar a kokarin ta wajen inganta tattalin arzikin kasa ta fuskar kasuwanci tsakanin kasashen ketare, samar da wadataccen abinci a kasa da kuma habbaka masana’antu.
Babban hafsan rundunar sojin yace taken taron ya zo a daidai kan gaba kasancewar bangaren sufuri baya samun kulawar da ta dace daga kwararru da malaman manyan makarantun kasar nan.
Laftanar Janar Yahaya ya lura da cewa bangaren sufurin kasar nan ya fuskanci kalubale da dama a shekarun da suka gabata da suka hada da rashin ingantattun kayayyakin aiki, rashin sanya idanu, rashin horaswa da sauran su.
Ya kuma jaddada aniyar rundunar wajen bada gudunmawa don ciyar da bangaren gaba.
Shima a nashi jawabin, Shugaban hukumar NIMASA, Dr Bashir Yusuf Jamoh wanda Farfesa Samuel Odewumi ya wakilta ya lura da cewa taken taron na bana ya maida hankali ne wajen inganta tsaro a bangaren sufurin kasar nan.
Ya kuma bukaci masu ruwa da tsaki a bangaren da suyi aiki tare wajen inganta bangaren sufurin yanda ya kamata.
A nashi tsokacin, Babban Sakatare a majalisar kula da sufurin jiragen ruwa na kasa Mr Emmanuel Jime wanda Mr C.C Agu ya wakilta ya ce hada-hadar sufuri ba zai yiwu ba, ba tare da samar da tsaro ba saboda sufuri wani kashin bayan tattalin arzikin kasa ne.
Ya kuma bukaci mahalarta taron da su lalubo hanyoyin da za su kara inganta da tsaftace bangaren sufurin kasar nan.
Sauran manyan bakin da sukayi tsokacin a wurin taron sun hada da Darakta Janar na hukumar cibiyar kimiyyar sufuri dake Zaria wato NITT, Shugaban kwalejin horas da matuka jiragen sama dake Illori, Kanar Yakubu Okatahi, wakilin gwamnan jihar Ogun da sauran manyan baki.
Taken taron shine Samar da kariya da tsaro a sha’anin sufuri a Nijeriya.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
Sharada Joins Kano Central Senatorial Race, Calls for Free and Fair APC Primaries
NEPC trains SMEs, MSMEs in Kano to boost export readiness
Traditional institutions key to security, peace building in Nigeria, security – CAS
Air Chief tasks commanders to decisive airstrikes against bandits, terrorists
Tinubu Meets Senator Sani Musa, Commends Support for Reform Agenda
Datti Baba-Ahmed Defects to PRP, Picks Membership Card in Zaria