Daga Abdullahi Kano
Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan Najeriya, Alhassan Ado Doguwa ya ce idan har ba ayi adalci ba jam’iyyar APC ka iya faduwa zabe a jihar Kano.
Jaridar Daily Trust ta rawaito Doguwa na fadin hakan ne yayin taron manema labarai da ya kira yau Talata a Kano bayan hargitsin da ya faru tsakaninsa da dan takarar mataimakin Gwamna na APC, Murtala Sule Garo.
Alhassan Ado ya tabbatar da cewa ba a gayyace shi taron masu ruwa da tsaki na APCn da aka gudanar a gidan mataimakin Gwamna Kano ba inda ya ce yaje ne domin ganin shugaban jam’iyyar Abdullahi Abbas
Sannan ya bayyana cewa zai ci gaba da baiwa jam’iyyar goyan baya tare da yin kira ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ya gaggauta shiga cikin rikicin kafin ya jawowa jam’iyyar Faduwa a zaben 2023.
“Muna fuskantar adawa wacce ba mu taba fuskantar irin fa”, inji shi yayin da yake bayanin irin yadda jam’iyyar NNPP ke kara habbaka a jihar Kano.
Duk wani yunkuri da majiyarmu tayi na jin ta bakin dan takarar mataimakin Gwamnan abin yaci tura.
Sai dai a zantawarsa da gidan rediyon BBC dan takarar mataimakin gwamnan na APC a Kano Alhaji Murtala Sule Garo yace yadda shugaban masu rinjayen yayi bayani ba haka lamarin yake ba,
“Yazo ya same mu muna taro yace baa gayyace shi ba, mai girma mataimakin gwamna yace ba shi ne ya zabi wadanda zasu halarci taron ba, gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne da kansa ya zabi wadanda zasu halarci taron.”
“Daga nan sai maganganu wanda har ta kaiga ya dauki kofin shayin da ke gaban Mai girma mataimakin gwamna ya jefe ni dashi.” Inji Muratala sule Garo

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
SPMC Begins Quarterly Oversight of Project Sites, Reviews Progress Across Zone 3
NGO trains girls on reusable pads, urges parents to prioritise girl-child education
Group demands full implementation of Katsina PWDs discrimination law
Jigawa to Provide Three Daily Meals for Pilgrims in 2026 Haj
Kano Police, NEMA Strengthen Partnership on Disaster Response
Kano Police Arrest Two Over ‘Aljannu’ Phone Scam, Recover 28 SIM Cards