Menu

Hon Kabiru Alhassan Rurum zai gwangwaje Alummar Rano,Kibiya ,Bunkure da sama da Naira Miliyan 22, Da buhunnan shikafa dubu daya don bikin Sallah

Admin 10 months ago

 

A Wani Abu da ba’a saba ganin masu rike da madafun iko (Zababbu ko Nadaddu) nayi ba, Dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure *RT Hon Kabiru Alhassan Rurum* ya fitar da kudi Miliyan 22 da dubu dari 5 da aka fara rabawa rukuni daban daban na Al’ummar kananan hukumomin sa a matsayin Barka da Sallah don suji dadin yin bukukuwan Sallah Babba..

Dan Majalisar ya Kuma fitar da Buhunan Shinkafa dubu 1 da za’a hadawa Mutane a wannan rabon saboda a girka abinci Sallah aci a baiwa makota..

Cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga Rurum din kan harkokin Yada Labarai Fatihu Yusuf Bichi ya fitar a litinan din nan yace ‘Dan majalisar yayi hakan ne da nufin Sanya farin cikin da Annashuwa a zukatan Al’ummar Mazabarsa tasa a wannan lokaci da ake Shirin yin Bikin sallah ga Kuma kakani kayin rayuwa da ake ciki.

Kowacce Karamar hukuma mutane 550 ne zasu amfana da kudaden da za’a raba Wanda a kananan hukumomin guda 3 ya kama zunzurutun kudi naira Miliyan 16 da dubu dari 5..

Akwai Kuma rukunin Matasa da ‘Yan Social Media da Mata da za’a rabawa wata naira Miliyan 2 sannan Kuma akwai Raguna guda 50 da aka siyo za’a rabawa Limanan Masallatan Juma’a na kananan hukumomin dan suyi layya.

Tuni Al’ummar Karamar hukumar Bunkure da aka fara rabon dasu a yau suka bayyana godiya da Jin dadinsu ga Dan Majalisar nasu da sukace baya gajiya wajen hidimta su…

Ko a lokacin Azumi kusan tan 6 na Shinkafa RT Hon Kabiru Alhassan Rurum ya rabawa Al’ummar kananan hukumomin nasa sannan a karshe ya bada Atamfofi da Shaddoji da kudin dinki ga fiye da mutane dubu 2 suyi shagalin Sallah…

*Fatihu Yusuf Bichi*
*Senior Special Assistant on Media & Publicity to Rt Hon Rurum*
*Member Representing Rano, Kibiya & Bunkure Federal Constituency, HOR Abuja.*
*June 2nd, 2025.*d