A cewar mai magana da yawun ɗan takarar gwamnan, Ibrahim Sani Shawai, Dr. Jamilu Gwamna gogagge ne ta fuskar aikin gwamnati da sanin harkokin tattalin arziƙi da zuba jari.
Shawai ya ce tattaunawa kan siyasar Gombe gabanin zaɓen 2027 bai kamata ta tsaya kan neman mulki da kalaman siyasa ba kawai, sai an duba ƙwarewar ƴan takara wajen tafiyar da tattalin arziƙin jihar, kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito.
”Gombe na buƙatar shugaba mai fahimtar zuba jari, kasuwanci, haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, samar da ayyukan yi da bunƙasa harkokin noma da fasahar zamani”. In ji shi.
Ya kuma bayyana cewa Jamil Gwamna ya taɓa zama Shugaban Hukumar Ruwa ta Jihar Gombe tare da samun gogewa a masana’antar rarraba wutar lantarki ta Najeriya.
Shawai ya ce irin wannan ƙwarewa za ta taimaka wajen sauya tattalin arziƙin Gombe daga dogaro da gwamnati zuwa tattalin arziƙi da noma, kasuwanci, fasaha, zuba jari wanda kamfanoni masu zaman kansu za su taka muhimmiyar rawa.
”Tambayar da ya kamata a yi a 2027 ba wai waye yake son zama gwamna ? ba ce, sai dai waye yake da ƙwarewar gudanar da gwamnati da tattalin arziƙin Gombe ?”, In ji shi.
Shawai ya kuma ƙara da cewa Dr. Jamil Gwamna na wakiltar shugabanci da ya ginu kan ƙwarewa, cancanta da hidimar jama’a.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Kabo Hon. Lawan Najume Kabo ya sauke Sakataren Mulki na Karamar Hukumar da nadaddun Kansiloli huɗu, Saboda Shiga Ƙungiyar Tallata Shugaba Tinubu Da Sanata Barau (TMS) a Jihar Kano .
Rabid dog bites 18 in Kano community
FGN/IFAD- VCDP, Taraba govt. move to boost personal hygiene for people with special needs
Kano Govt Suspends Durbar, Horse-Riding Activities Over Security Concerns
Guwor: Tinubu’s Reforms Attracting Support Across Nigeria
Jigawa Hisbah Arrests Eight Over Alleged Homosexual Acts
Kano Govt Approves N144bn For Development Projects