Menu

AN YABAWA HUKUMAR NIMASA BISA TAFIYA DA MATA

Admin 3 years ago

Jami’ar harkokin sufurin jiragen ruwa ta duniya ta yabawa hukumar NIMASA bisa tafiya da mata da kuma basu damar baje fasahar su ta hanyar tura su kasashen ketare don karo ilimi.

A wata sanarwar da mataimakin darakta a sashin hulda da jama’a a hukumar, Mr Edward Osagie ya rabawa manema labarai a birnin Ikko yace yabon ya fito ne daga bakin Shugabar Jami’ar, Dr Cleopatra Doumbia-Henry a lokacin da ta kawo ziyara a shedikwatar hukumar don tattaunawa akan batun inganta horas da ma’aikatan NIMASA.

Dr Cleopatra Doumbia-Henry tayi bayanin cewa maqasudin ziyarar ita ce don karfafa hadin gwiwa tsakanin jami’ar da NIMASA da kuma lalubo sabbin hanyoyin kyautata dangantaka.

Shugabar Jami’ar har ila yau ta kuma yaba da karin mata da aka tura su jami’ar don zurfafa ilimin akan harkokin sufurin jiragen ruwa.

A nashi bangaren, Shugaban hukumar kula da iyakokin ruwan kasar nan, Dr Bashir Yusuf Jamoh yace dadaddiyar alaqar dake tsakanin hukumar da jami’ar ta samo asali ne bisa ga burin da hukumar take da shi wajen inganta kwarewa ta fuskar bincike don don ciyar da hukumar gaba.

Ya kara da cewa hukumar na da burin cigaba da karfafa gwiwar mata shiga a dama da su a bangaren harkokin iyakokin ruwa da kuma sufurin jiragen ruwa.

Dr Bashir Jamoh ya jaddada aniyar hukumar wajen cigaba da horas da ma’aikatanta don inganta kwarewar jami’an ta a bangaren iyakokin ruwan Nijeriya.