A kudirinta na ganin yan Nijeriya sun mallaki jiragen ruwa cikin sauqi, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da gagauta bada bashi ga yan kasa masu ra’ayin mallakar jiragen ruwa.
Ministan harkokin sufuri, Injiniya Mu’azu Jaji Sambo ne ya bayyana haka a wajen taron manema labarai inda ya ce an amincewa bankunan Union, Zenith, Polaris, UBA da Ja’iz a matsayin cibiyoyin da za su rarraba kudaden.
Ministan yayi nuni da cewa ma’aikatar shi ta fara tuntubar Ministar kudi, da Gwamnan babban bankin Nijeriya don fara aiwatar da tsarin.
Ya kuma bayyana fatan cewa wannan tsarin zai kara bunkasa hada-hadar sufurin jiragen ruwa a bangaren iyakokin ruwan kasar nan.
A nashi tsokacin Shugaban hukumar kula da iyakokin ruwan kasar nan Yusuf Jamoh yayi bayanin cewa kudaden da aka amince a bada rance sun haura sama da naira miliyan dubu goma sha shida, sai kuma kimanin dala miliyan dari uku da hamsin.
Shi dai wannan tsarin an fara shi ne a shekarar 2003 don karfafawa gwiwar yan Nijeriya su mallaki jiragen ruwa don gudanar da kasuwanci inda za su biya kashi goma sha biyar, ita kuma hukumar NIMASA ta bada kashi talatin da biyar, sai kuma bankuna su bada kashi hamsin.

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
Ambassador Dr. Amina Umar Namadi: A First Lady Defined by Compassion, Service, and Humanity
Police Rescue Abducted Three-Day-Old Baby, Arrest Two Suspects in Nasarawa
Governor Yusuf Mourns Alhaji Nuhu Dantani
ADC Leaders Reject INEC Decision, Vow to Resist, Mobilise Support in Otukpo
Police Disburse ₦9.26m to Families of Fallen Officers in Kano