Menu

An Kaddamar da Titi Mai Sunan Marigayiya Hanifa a jamiar MAAUN

Admin 4 years ago

Daga Sufi

Shugaban Jami’oin Maryam Abacha American University Dake Nigeria da Niger ya kaddamar da karramawar ha Marigayiya Hanifa Abubakar Abdulsalam da katafaren Titin dake cikin Jami’ar dake a nan Kano wanda aka sa sunan ta.

A wajen kaddamawar Akwai Iyayen marigayyar da ‘yan uwan na Hanifa tare da wasu Turawa da ga wasu jami’oi a kasar Ukraine da suka Kawo ziyara Jami’ar.

Mahaifin Hanifa ya nuna farin cikin sa da wannan Karramawa da akayi Masu da fatan Allah ya saka da kuma rokon Allah ya jikan ta Amin.

Prof. Gwarzo ya jaddada damuwar sa na rashin Hanifa da kuma niyyar sa kan kaddamar da titin don tunawa da Marigayiya Hanifa da nuna yadda Abin ya shafe shi da duniya Baki daya.

Ya kuma yi adduar Allah ya sa mai ceto ce ya kuma kara musu hakurin rashin ta Amin.