Aisha Dorayi
Al’ummar ƙaramar hukumar Ungogo a jihar Kano sun yi zargin shugaban ƙaramar Abdullahi Garba Ramat da ya sayar da filin asibitin larurar kuturta na Yadakunya da aka fi sani da asibitin Bela.
Asibitin na Bela wanda Turawa ne su ka gina shi fiye da shekaru 60 da nufin samarwa da masu cutar kuturta da masu larurorin fata gurin neman magani na musamman.
Sai dai kuma ana zargin Abdullahi Garba Ramat da sayar da gidajen da ake ajiye marasa lafiya da kuma wani ɓangare na filin asibitin, inda aka canza musu da wani guri mai nisa da asibitin.
Haka kuma wani bincike da jaridar Sahelian Times ta yi ya bayyana cewa iya filaye goma (10) kacal aka baiwa waɗanda abin ya shafa, inda aka haɗa mutum huɗu a fili ɗaya su raba.
Haka kuma dagacin Yadakunya Malam Zubairu Sulaiman ya koka akan wannan al’amari. Inda ya ce fili mai faɗin kafa arba’in (40) ya yi musu kaɗan.
Malam Zubairu Sulaiman ya ce ƙara da cewa ƙaramar hukumar Ungogo ta ba su filaye 10 ne kacal, wanda su kuma adadinsu ya kai fiye da iyalai 30.
Wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa sun bayyana damuwarsu akan yadda za su iya samun kuɗin da za su gina wannan fili da aka ba su a maimakon gidajen da su ke ciki.
“Mafi yawan mu sai mun fita bara sannan mu ke samun abin da zamu ci mu da iyalanmu, dan haka ta yaya ake tsammanin zamu samu kuɗin da za mu gina wadannan filaye?”.
Kabiru Adamu, wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa ya bayyana cewa mafi yawansu sun dogara ne daga abin da jama’ar gari su ke ba su a matsayin sadaka, kuma yanzu gashi an kai su nesa da al’umma.
“Rayuwar ta yi tsananin a garemu” In ji Kabiru Adamu.
Lokacin haɗa wannan rahoton shugaban ƙaramar hukumar Ungogo, Abdullahi Garba Ramat bai samu damar ɗaukar waya ba
Asalin Labari….Jaridar labarai 24

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
Traditional institutions key to security, peace building in Nigeria, security – CAS
Air Chief tasks commanders to decisive airstrikes against bandits, terrorists
Tinubu Meets Senator Sani Musa, Commends Support for Reform Agenda
Datti Baba-Ahmed Defects to PRP, Picks Membership Card in Zaria
AI crucial for accountability in Nigerian varsities, says EFCC Chairman
National Development: Emir Sanusi urges universities to drive AI policy