Menu

Ku Kara Hakuri Maaikata, Muna Sane da Halin da ku ke Ciki – Kungiyar Kwadagon Jihar Kano

Admin 4 years ago

kungiyar Kwadago ta kasa reshen jihar Kano ta ce tana sane da rashin biyan ma’aikata hakkokin su na watan Afirilu Lamarin daya jefa su cikin kuncin rayuwa.

Shugaban kungiyar Kwamared Kabiru Ado Minjibir ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar.

Acewar sa suna sane da halin da ma’aikatan suka shiga sakamakon rashin albashin kasan cewa galibin su sun dogara ne da albashi wajen shidimar sallah.

Kwamared Ado Minjibir ya bukaci ma’aikatan su kara hakuri zasu warware matsalar duk da ma’aikatan sun ta bayyana halin da suke ciki a kafafen sada zumunta.