Menu

Hada ayyukanmu wuri guda a matakin kasa shi ne burinmu- Hukumomin sa ido kan sufuri.

Admin 4 years ago

•Saura kiris mu mayar da ayyukanmu ta amfani da na’ura mai kwakwalwa. – Shugaban NIMASA

Hukumomin gwamnatin tarayya karkashin inuwar ma’aikatar sufuri ta tarayya (FMOT), sun cimma matsayar daidaita tsarin su na cikin gida, tare da ci gaba da mai da hankali kan aiwatar da tsarin bai daya a matakin kasa a fannin sufurin kasar nan. An cimma wannan yarjejeniya ne a taron shugabannin hukumomin sufuri karo na 4 da aka yi a Legas.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan kammala taron, magatakardar hukumar kula da harkokin jigilar a Najeriya (CRFFN), Barista Sam Nwakohu, ya bayyana cewa, yin cikakken tsarin amfani da naura mai kwakwalwa wurin tafiyar da harkokin cikin gida na hukumomin daban-daban da suka sanya hannun a yarjejeniyar, wani abu ne da ya ke da muhimmanci gabanin a iya samun matattarar bayanai a wuri guda a matakin kasa.

Nwakohu, wanda shi ne Shugaban taron, ya ce manyan jami’an gudanarwa na hukumomi daban-daban sun amince da lokacin da za su zamantar da ayyukansu. “Mun amince da cewa dukkan Hukumomin da ke karkashin Ma’aikatar Sufuri ya kamata a matsayin fifiko, su zamanantar da ayyukansu ba tare da bata lokaci ba. Wannan tsari za a daidaita shi da kyau kuma mun kuma ba kanmu jadawalin lokaci don cimma wannan. ” Yace.

A nasa bangaren, babban daraktan hukumar kula da harkokin jiragen ruwa ta Najeriya NIMASA, Dr. Bashir Jamoh ya bayyana cewa shirin zamanantar da ayyukan Hukumar NIMASA don amfani da fasahar zamani sun kai sama da kashi 80%.

Jamoh ya kuma ba da tabbacin cewa NIMASA ta himmatu wurin rungumar tsarin zamani ne don takaita ayyakunan mutane, tare da toshe ɓarnar kudaden shiga a cikin tsarin. “A daidai da dokar da gwamnatin tarayya ta bayar na saukaka harkokin kasuwanci, mun himmatu wajen samar da cikakken aiki na yanar gizo don samun rage yawan mu’amalar da masu ruwa da tsakin mu kuma hakan yana cikin kokarinmu na tabbatar da gaskiya da sanin yakamata wanda bangaren ke bukata. Manufar ita ce a daidaita da shirin a matakib kasa domin ya zame na daya, lokacin da aka kammala dukkan ayyukan cikin gida na hukumomi daban-daban,” in ji shi.

Da yake tsokaci game da hauhawar kudin dakon kaya kuwa kan jiragen ruwa na Najeriya; Shugaban NIMASA ya bayyana cewa hukumar za ta mayar da hankali wajen wayar da kan jama’a, tare da zage damtse ga kasashen duniya domin yin nazari. Wannan mataki dai na da nasaba ne da fitar da Najeriya daga jerin masu fashin teku a duniya.

“Zai iya ba ku sha’awar sanin cewa zuwa ƙarshen wannan kwata, wato ƙarshen watan Yuni, da mun sake yin wani sabon tarihi domin har yanzu ba mu sami wani hari ko wani lamari na rashin tsaro a teku a cikin ruwanmu ba. Don haka, za mu ci gaba da bayar da shawarwarin kawar da Inshorar Hadarin Yaki da kasashen duniya baki daya, domin ‘yan Nijeriya su ci gajiyar hakan,” in ji Jamoh.

Za a iya tunawa cewa bugu na farko na taron ya kasance a cikin 2020, da nufin haɓaka aiki tare da haɗin gwiwar hukumomi na maaikatar sufuri , wanda aka yi niyya don ingantacciyar sashin teku mai inganci.

Taron kuma ya samu halartar; Manajan Daraktan Hukumar Tashoshin Ruwa ta Najeriya (NPA), Mista Mohammed Bello Koko; Babban Sakataren Hukumar Kula da Jiragen Ruwa ta Najeriya (NSC), Hon. Emmanuel Jime; Manajan Darakta, Hukumar Kula da Ruwayen kasar nan (NIWA), Dr. George Moghalu.

Sauran su ne; Manajan Darakta, hukumar sufurin jiragen kasa (NRC), Mista Fidet Okhiria; shugaban makarantar Maritime Academy of Nigeria (MAN) Oron, Commodore Emmanuel Duja Effedua da Darakta Janar na Cibiyar Fasahar Sufuri ta Najeriya (NITT), Zaria, Mista Bayero Salih-Farah Zaria.