Menu

Shugaban NIMASA ya taya ‘yan Najeriya murnar Babbar Sallah

Admin 4 years ago

Shugaban hukumar kula da sufurin jiragen ruwa na kasa, NIMASA, Dr. Bashir Yusuf Jamoh ya taya daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar bikin babbar sallah Eid El Kabir.

A sakon da ya bayar da aka rabawa manema labarai, Dr. Jamoh ya Kori musulmi da suyi amfani da wannan lokaci wajen ribanya addu’o’i ga kasa don magance matsalolin da suka addabi najeriya.

Ya kuma roki mabiya addinin musulunci da na kirista da su cigaba da zama lafiya da fahimtar juna ba tare da nuna Wani bambanci ba.

Shugaban na NIMASA ya jawo hankalin ‘yan najeriya musamman wadanda suka Isa kada kuriah da suyi kokarin mallakar katin zaben su ganin hukumar zabe,INEC ta Kara lokaci domin haka.

Ya kuma gargadi jama’a da kada su yarda ‘yan siyasa su sayi ‘yancin su ta wajen Basu kudi don su yi zabe. Inda ya hore su da su tabbatar sunyi zabe bisa chanchantar don samun cigaba Mai ma’ana.

Dr. Jamoh sai ya gargadi matasa da su kaucewa shiga bangar siyasa ko ta’addanci don samun nasarar zabubbukan da ke gaba.

Shugaban NIMASA ya roki mahajjata da ke aikin Hajji a kasa Mai tsarki, da su dukufa wajen yiwa kasa addu’a don magance matsalolin tsaro da na tattalin arzikin kasa.

Sai kuma ya taya shugaban kasa, Muhammad Buhari da Ministan sufuri murnar shagulgulan Sallah tare da fatan Allah Ya maimaita.