.. YA BAWA MATASA TABBACIN BARIN TARIHI MAI KYAU DA GWAMNATI MAI TAFIYA DA KOWA.
Dan Takarar shugabancin Najeriya na Jam’iyyar PDP a zaben 2023 kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bawa matasan Najeriya tabbacin barin kyakkyawan tarihi gare su, idan aka bashi damar jagorantar al’amuran kasar.
Atiku Abubakar ya bada wannan tabbaci ne yau Laraba 3 ga watan Agusta, Lokacin da ya karbi bakuncin tawagar shugannin PDP sabon karni karkashin jagorancin babban daraktan ta Audu Mahmud a gidan sa dake Abuja.
Dan Takarar shugabancin kasar ya sake jaddada aniyar sa kamar yadda ta ke kunshe cikin kundin manufofin sa, na bawa matasa dama a gwamnatin sa ta hanyar ware musu kaso 40, inda kuma yace zai yi sauye-sauyen da suka Kamata domin bada dama ga mata da matasa.
Wazirin Adamawa ya kara da cewa a gwamnatin PDP ne kawai aka aiwatar da tsarin nan na kebewa mata kaso 35, inda yace APC ba ta taba girmama wannan yarjejeniya ba.
Ya kuma koka game da halin da matasa suka sami kansu, inda ya yi alkawarin daidaita al’amuran. A saboda haka, yace ilimi zai zamo babban ginshikin gwamnatin sa domin bunkasa rayuwar matasa da habaka dimukuradiyya. Ya bayyana takaici kan yadda APC ta wargaza tsarin da gwamnatin PDP ta shimfida a baya.
Yayin da yake tabbatar da muhimmancin matasa Wajen Gina kasa, Dan Takarar na PDP ya jaddada cewar zai yi aiki da bukatun zamani, tare da gudanar da gwamnati Mai tafiya tare da kowa Mai la’akari da banbance-banbancen dake tsakanin mu.
A nasa jawabin, jagoran ayarin, Audu Mahmud yace Atiku Abubakar wata mabubbuga ce ta karfafa gwiwa da kyakkyawan tunani ga matasan kasar nan, inda ya bayyana yakinin da yake da shi na kwarewar Atiku domin magance matsalolin tattalin arziki da matsalolin siyasa domin amfanin dukkan yan Najeriya.
Abdulrasheed Shehu
Mataimaki na Musamman ga Mai girma Atiku Abubakar kan kafafen yada labarai.
3 ga Agustan 2022.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
Traditional institutions key to security, peace building in Nigeria, security – CAS
Air Chief tasks commanders to decisive airstrikes against bandits, terrorists
Tinubu Meets Senator Sani Musa, Commends Support for Reform Agenda
Datti Baba-Ahmed Defects to PRP, Picks Membership Card in Zaria
AI crucial for accountability in Nigerian varsities, says EFCC Chairman
National Development: Emir Sanusi urges universities to drive AI policy