Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen Jihar Yobe ta kama mutum uku da zargi da fashi da makami da fasa gida domin sata.
A wata sanarwa da mai magana da yawun yan sanda reshen Jihar Yobe ASP Dungus Abdulkarim ya fitar, cikin wadanda ake zargi har da wani soja da ke ƙarƙashin rundunar Operation Hadin Kai.
Tunda farko mutanen uku dai sun fasa gidan wata mata a Sabon-Pegi da tsakar dare dauke da muggan makamai ciki har da bindiga ƙirar AK-47 inda suka sace kudi kimanin naira 250,000 haka kuma suka sace mota ƙirar Peugeot 307 da wayar salula Nokia.
Sai dai bayan ƴan sanda sun samu labarin wannan lamari, sai suka shiga aikin nemansu har suka kama su.
Tuni waɗanda ake zargin suka amsa laifukan da ake zarginsu da aikatawa

Amincin Tinubu Ga Barau Kan Harkar Tsaro Da Cigaban Kasa
Shugaban Ƙaramar Hukumar Kabo Hon. Lawan Najume Kabo ya sauke Sakataren Mulki na Karamar Hukumar da nadaddun Kansiloli huɗu, Saboda Shiga Ƙungiyar Tallata Shugaba Tinubu Da Sanata Barau (TMS) a Jihar Kano .
Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Kano Govt Says 55.7% of 1,557 Projects Completed
Kano Pilgrims Welfare Board Announces N7.67m 2027 Hajj Fare
Kano Information Commissioner Wins National Crisis Communicator Award
Kano Police Arrest Five Suspected Armed Robbers, Recover Illegal Firearm
Tinubu Trusts Barau To Speak on Security, Development at a Summit