Darakta-Janar na hukumar kula da harkokin sufurin jiragen ruwa ta Najeriya, Dr Bashir Yusuf Jamoh, ya ce har yanzu bai fito fili ya bayyana aniyarsa ta takarar gwamnan jihar Kaduna a hukumance ba.
Sai dai shugaban ya bayyana cewa bai kawar da yiwuwar yin aiki da kiraye-kirayen mutanensa ba idan sun ga ya dace ya tsaya takarar.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai a Zariya, Dr Jamoh ya ce ko da ya gamsu ya tsaya takarar ‘ba na a mutu ko a yi rai ba ne’.
Shugaban ya ce, “Ba zan nace cewa dole ne in zama gwamna ‘ko ana ha maza ha mata ba’. Amma zan so in yi wa jama’ata hidima kuma in kai ga iyakar abin da suke tsammani.”
Ya kara da cewa mutane da kungiyoyi da dama daga kananan hukumomi 23 na jihar suna ci gaba da tuntubar sa domin ya tsaya takara.
Dr Jamoh ya ce nan ba da jimawa ba za a bayyana matsayinsa idan ya kammala shawarwarin nasa.
Shugaban NIMASA ya ci gaba da cewa abin da gidauniyarsa ke yi ya bambanta da duk wani buri na siyasa, kamar yadda aka yi a cikin shekaru biyu da suka gabata.
“Jamoh Foundation na da burin inganta zamantakewar jama’a musamman ma wadanda aka zalunta a matsayin hanya ta na tallafaw jama’a kamar yadda suka Dade suna yi min kara.
“Gidauniya tana bayar da tallafin ilimi ga matasa, gudanar da aikin jinya da bayar da tallafin noma ga ‘yan kasa,” in ji shi.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
NSSF charges schools on sportsmanship
Governor Radda Declares War on School Violence, Launches Protection Policy
APC Aspirant Gumel Submits Nomination Forms for Reps Seat
Gumel: Retired DIG Denies Accepting Consensus Process for 2027 Reps Race
Taraba 2027: Why we must take back our state from vampires—Sen Bwacha
Masha Allah, muna bayanka, hundred percent Inshaallahu